Bayan labarin cewa ya saki matarshi: Adam A. Zango ya saiwa matar tashi sabuwar mota


A makon da ya gabata ne mujallar Fim Magazine ta ruwaito cewa, tauraron fina-finan Hausa kuma mawaki, Adam A.

Zango ya saki matarshi, labarin da ya dauki hankulan mutane sosai musamman masoya fina-finan Hausa to saidai da safiyar yau, Lahadi, Adamun yace ya sayawa matarshi sabuwar mota.

Badai aji komai ba daga Adamu akan labarin sakin matarshi da ya watsu ba
Masu iya magana na cewa tsakanin mata da miji sai Allah, a cikin wani labari da ya wallafa da safiyar yau, Lahadi, Adam A.

Zango ya bayyana cewa ya saiwa matarshi sabuwar mota.

Wannan bayani ya dauki hankulan mutane inda wasu ke tambayar to in maganar cewa ya saki matarshi da akayi?.

Abinda zamu ce dai anan shine Allah ya kar dankon soyayya.

Ga hoton motar.

Source: https://ift.tt/2x17dHrTallata wakar ka : Send Email Or Call