Priyanka Zata auri Kanninta

Shahararriyar Jaruma Yar kasar India,  Priyanka Chopra zata auri wani matashin mawaki wanda ta girme masa da shekara 11.

Mawakin dan Asalin kasar Amurka mai suna Nick Jonas ya fara waka tun yana shekara 7 ya saki album dinsa na farko a 2002.

Jarumar wacce yanzu ta maida akalar harkokin fina-finanta ga masana'antar Hollywood dake kasar Amurka, duk da cewa a kwanaki aka shirya fitowarta a wani fim tare da Jarumi Salman Khan inda daga baya ta Janye daga fim din.  Tun daga lokacin aka fara Rade-Radin cewa tayi haka ne saboda auren da take shirin yi.

Priyanka da Nick sun hadu a yan watannin da suka wuce inda hakan yake ba mutane da dama mamaki.

Duk dai ba'a bayyana ranar daurin auren ba,  amma anyi bikin sa rana kamar yanda al'adar kasar india ta tanada.  Bikin wanda ya samu halartar iyayen Nick da Priyanka da kuma yan'uwa da abokan arziki ya gudana a ranar Asabar 18/08/2018. A garin mumbai. 


Source: https://ift.tt/2PnRnhJTallata wakar ka : Send Email Or Call