Mahaifiyar Nafeesa Abdullahi ta rasu

Innalillahi wa inna ilaihi raji'un.
Tauraruwar fina-finan Hausa, Nafisa Abdullahi tayi rashin mahaifiyarta a ranar Talata, kamar yanda ta bayyana, tace, mun rasa komai a yau amma Allah yafi mu sonki dan haka zamu biki da addu'a.

Nafisar ta kuma yi kira ga masoyanta da su saka mahaifiyar tata cikin addu'o'insu.

Sannan tayi Alkawarin fara lissafi daga yau har randa zata hadu da mahaifiyar tata a Aljannah, kamar yanda ta bayyana,

Har yanzu dai ana cigaba da yi ma Jarumar ta'aziyya daga abokan aikinta zuwa masoyanta da kuma abokan arziki. 


Source: https://ift.tt/2OBH6x0Tallata wakar ka : Send Email Or Call