Fim Din ‘In Search Of The King’ Ya Samu Goyon Bayan Masarautar Ringim

In Search Of The King

A farkon watan Yuli aka shiga aikin wani fim na turanci mai suna In Serach of the King, wanda yake ba da tarihi da yanayin masarautar Kasar Hausa tun tsawon shekaru masu yawa da suka gabata.

Duk da cewar fim ne da aka yi shi da harshen turanci amma idan ka dauke yaren na turanci da aka yi amfani da shi, to duk wani abu da aka nuna a fim din yana nuna ydda tsarin rayuwar masarautar kasar Hausa take ta fannin al’adu, ilimi, mulki da mu’amalarsu ta yau da gobe.

Wani abin birgewa game da wannan fim din kusan za a iya cewa shi ne fim na farko da aka nuna yadda Sarautar kasar Hausa take a zahiri, ba wai kwaikwayo ba. Domin kuwa an yi amfani da gadon sarautar Ringim ne inda Sarkin na Ringim dake jihar JIgawa ya amince a yi aikin fim din a masarautarsa kuma ya bayar da aron duk wata fada da ake bukata domin gudanar da ikin fim din.

Kuma ya ba da mutanesa da suka rinka kula da aikin don su tabbatar an bi tsarin sarautar ba tare da an yi mata kutse ba, kamar yadda aka saba yi a sauran finafinan da ake yi a Kannywood.

Fim din dai labarin masarautu ne masu karfi har guda uku a kasar Hausa kuma Ali Nuhu da Yakubu Muhammad da Abba Almustapha suka fito a matsayin sarakuna. Sai Nafisa Abdullahi da ta fito a matsayin Gimbiya kuma jarumi mai tasowa Abdullah Amdaz ya fito a matsayin Yarima.

Kabiru Musa Jammaje shi ne ya dauki nauyin shiryawa.

Ganin yadda fim din ya samu amincewa ga masauratar Ringim har aka yi aikin a cikin fadar, mun tambayi jagoran shirin Malam Kabiru Jammaje a game da matakan da suka bi har suka samu amincewar masarautar da kuma yadda aikin ya gudana.

Inda ya shaida mana cewar, “Tun da farko ma dai da muke yin aiki a kan rubuta labarin, gaskiya ba mu dauka za mu je har Ringim domin yin aikin ba, saboda a tunaninmu za mu samu wajen da za mu yi aikin a kusa, sai ya zama mun je gurare da dama amma sai muka ga bai yi mana yadda muke so ba, don haka sai aka kawo shawarar a tafi wajen Sarki Ringim za a iya samu.

Don haka da muka je muka yi gaisuwa kuma sai muka ba da takardar neman izini ta a ba mu dama mu yi amfani da masarautar don gudanar da aikin, kuma abin farin ciki suka nuna goyon baya suka aiko mana da takardar amincewa ta hannun Danmajen Ringim.
Kuma wani abu a ya zo mana bazata wanda ya kara inganta mana aikin shi ne yadda masarautar ta ba mu mai kula da mu ya kasance tare da mu wato Yariman Ringim.

Don sun ce suna kallon finafinai da ake yi na sarauta, amma ba a nuna masarautu yadda ya kamata, don haka tun da a masarautarsu za a yi ba za su zuba ido su ga an murguda yadda tsarin masarauta yake ba, don haka ba biyan su muka yi ba sune suka ga dacewar yin hakan, don suna daukar cewar wani nauyi ne a kansu musamman da muka nuna musu cewa fim din za a yi shi da turanci ne kuma zai shiga kasashen Turai da ma wasu nahiyoyi na duniya, don haka suka ga hakkinsu ne su tsaya su tabbatar an yi tsarin sarautar da ta shafi Arewacin Najeriya yadda ya kamata.

Nafisa Abdullahi ita ce jarumar da ta fito a matsayin Gimbiya a fim din, ta bayyana cewa, “Duk da cewar wannan fim din ba shi ne na farko da nake fitowa a cikin sarauta ba, to shi wannan ya zo mini da siffa ta daban, kasancewar sa na Turanci. Don haka a nan zan iya cewa In Search of the King ya bambanta da sauran finafinan da na saba fitowa, kuma aikin ya burge ni sosai don na ji dadinsa.”

Shi ma jarumin fim din Abdullahi Amdaz wanda ya kasance fim din ne na farko a gare shi da ya zamo babban jarumi, ya shaida mana cewar, “Na yi farin cikin kasancewa a matsayin jarumin wannan fim din, “Duk da cewa shi ne fim na farko da na zamo babban jarumi a cikinsa. Don haka sai na ji a zuciyata zan yi kokari na yi duk wani abu da zai ba da fa’ida kuma ya fito da kima da darajar aikin. Na fito a matsayin Bello da ya ke yawo a tsakanin masarautu guda uku domin neman cimma wani burina kuma a hakan na samu kaina a yanayi kala-kala don na samu na yi.”

Zuwa yanzu dai an kammala kashin farko cikin kashi uku na fim din har an tafi hutu, sai a watan Oktoba za a ci gaba da kashi na biyar da na uku a garin Kano da kuma Danbatta.

Fim din dai ya kunshi jarumai masu yawan gaske da suke aiki a cikin fitattun ‘yan Kannywood akwai Ali Nuhu, Abba Almustapha, Yakubu Muhammad, Nafisa Abdullahi, Rabi’u Rikadawa, Rukayya Dawayya, Shehu Hassan Kano, Shu’aibu Yawale, Tijjani Faraga da sauransu.Tallata wakar ka : Send Email Or Call