Zamu kawar da su Hadiza Gabon da Jamila Nagudu inji wani Director

Zamu kawar da su Hadiza Gabon da Jamila Nagudu

Za Mu Ture Jarumai Irinsu Jamila N. Da Hadiza G. Mu Kawo Sabbin Jini, Inji Darakta Aminu S. Bono

Shahararren mai bada umarnin nan na finafinan Hausa Aminu S. Bono ya bayyana kalubalen da masana`antar shirya finafinan Hausa ta Kannywood ke fuskanta da cewa karancin jarumai mata masu jinni a jiki.

A cewarsa masu kallon finafinan mu na yi mana kallon mahaukata idan muka sanya fuskokin jarumai mata irin su Hadiza gabon, Fati Washa, Aisha Tsamiyya, Jamila Naguda DS, amtsayin yan mata musamman ma na kauye, saboda yanzu fuskokinsu sun koma na iyeye ba yan mata ba.

Al`adarmu ta bahaushe ba ta yi daidai da ganin gandama gandaman yan mata irinsu a kauye ba a matsayin yan mata, saboda haka kallubalen masana`antar shine “newfaces”wato sabbbin jarumai masu tasowa irinsu Maryam Yahaya, Bilkisu Shema, Zulaihat Ibirahim,Zee Pretty, Amal Umar da sauransu.

“Amma yanzu jaruman da muke da su kamaninsu duk sun juye sun koma na tsofaffi kon kuma wasu iyaye, Sai dai matsalar mu da muka fuskanta a baya nada nasaba da karancin rashin hanyar fito da jaruman da za su maye gurbin tsofaffin da kullum masu kallon fuskarsu suka fara kosawa da su, saboda haka muka yi tunanin kawo sabbin jarumai ta hanyar da mutane suka fi so wato nishadi kamar ta hanyar wakokin bidiyo da ba a saba da su cikin finafinai ba.
Tallata wakar ka : Send Email Or Call