Mutuwa Ce Za Ta Raba Ni Da Kwankwasiyya Inji Mustapha Nabraska

Nebraska

Mutuwa Ce Za Ta Raba Ni Da Kwankwasiyya Inji Mustapha Nabraska


Daga Aliyu Ahmad

Fitaccen jarumin finafinan Hausa, wanda kuma dan gani kashe nin tsohon gwamnan Kano,  Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ne, wato Mustapha Nabrask ya karyata rade-redin da ake na cewa ya sauya sheka daga Kwankwasiyya zuwa Gandujiyya.

A zantawar Nabraska da RARIYA, ya bayyana cewa hotunan da ake ta yadawa cewa ya yi wa Gandujiyya mubaya'a, ba gaskiya ba ne, kawai sun hadu ne da mutanen gwamantin Kano a wurin zaben shugabannin jam'iyyar APC na kasa da ake gudanarwa a Abuja. Kuma sun kira shi domin a gaisa kasancewar sa dan Kano.

"Sun kira ni ne muka gaisa, har suke zolaya ta cewa har yanzu na ki bin su a tafi tare a siyasa, sai nake ce musu ai siyasa kowa yana da ra'ayinsa. Don haka ni Kwankwaso zabina, kuma bai mu raba ni da shi", cewar Nabraska.
Tallata wakar ka : Send Email Or Call