Majalisar Ɗinkin Duniya Ta Karrama Rahama Sadau

Majalisar ɗinkin duniya ta karrama Rahama Sadau

Majalisar Ɗinkin Duniya Ta Karrama Rahama Sadau

Kamar yadda jarumar ta wallafa a shafin ta na Instagram jarumar tace

An karramani ne a daren jiya, cikin bikin film na mata, wanda ya dace da Majalisar ɗinkin duniya, ina da matuƙar ƙwarewa sosai,

Kuma ina mai matuƙar farin ciki da kasancewa ta cikin sahun mata masu ƙwarewa da ban mamaki  da aka karrama

Haƙiƙa a wasu lokuta a rayuwa, idan na tsaya na tambayi kaina, sai na riƙe cewa wai shin ma har da yaushe na isa nan

To haƙiƙa babu shakka wannan na ɗaya daga cikin lokutan da bazan taɓa manta wa ba a rayuwa, na gode sosai

To kunfa ji dama ita ɗauka ka, a bace ta Allah, kuma ya kan bada ita a duk lokacin da ya so, kuma ga duk wanda ya so, domin haka ita hassada ba komai bace illa face taki ga duk wanda Allah ya nufa da babban rabo a rayuwa

Yau dai gashi barin Rahama sai cika yake yi kamar yadda ta sha faɗi babban barin ta a rayuwa shine taga ta zama cikakkiyar jarumar film ta duniya, kuma gashi Alhamdulillah ta zama

Sai dai fatan mu anan shi ne Allah ya kare ta daga dukkan sharrin mai sharri, ya kuma kare ta daga sharrin shaiɗan ya kuma bata ikon kiyaye iyakokin addinin ta Ameen,

Domin haka mu Hausawa ne, kuma muna son ci gaban namu aka ina yake a faɗin Duniyar nan, domin haka muna yiwa Rahama Sadau fatan Alkhairi

Tallata wakar ka : Send Email Or Call