Ali Nuhu da Adam A Zango duka Azzalumai ne inji Ali Artwork

Ali Nuhu da Adam A Zango duka Azzalumai ne inji Ali Artwork

Ali Nuhu da Adam A Zango duka Azzalumai ne inji Ali Artwork


Sakamakon wani sabon rikicin daya ɓarke ƙwanan nan, tsakanin fitattun jaruman Kannywood guda biyu Ali Nuhu da Adam A Zango

Hakan ne yasa magoya bayan jaruman biyu keta cece kuce harma da gore gore a kafafen sada zumunta

Inda shi kuma fitaccen Matashin nan da akafi sani da Ali Artwork yayi wa duka jaruman biyu wankin bargon tsohuwa inda ya nuna cewa dukkan su azzalumai ne a masana'antar Kannywood,

Kuma ko wanne daga cikin su yayi aiki dashi, amma babu wani abun azo a gani da suka tsinana masa

Gadai abunda Ali Artwork ɗin ya rubuta a shafin sa na sada zumunta na Instagram


Duk abunda kuka GA sunayi suna sane kuma su suke kirkirar hakan don su motsa jam'iyya kar a ce ai kwana biyu an manta da su to ku sani ku Masoyansu ku suka mayar mahaukata in baku manta ba a shekaru baya suntaba shirya irin wannan rikicin nasu mu kazo mukai ta cecekuce a kai

Amma daga Karshe mai hakan ta haifar sai suka maidamu bamu san komai ba Dan haka kusan duk wanda yasa kansa sai yayi dana sani ni yanzu babu ruwana da kowa a cikinsu dan ba wanda a cikinsu zai iya kashe min matsalar dubu 200,000 kowa a cikinsu na zauna da shi ba wanda bai moreniba akan harkata ta editing

Amma babu wanda na taba WA aiki ya dauki dubu dari 100,000 ya bani in kuma da akwai ya fito ya karyatani sai dai kai ta bautar banza sun fiso kullum kai ta basu girma suna zalintarka to ku sani anyi walkiya munga kowa

#Kyar_Nake_Kallonku ba ruwa na da rigimar wani ni ma takaina nake in kanayi dani inayi da kai in bakayi dani nima baruwa na dakai ku kuma Ali da Adamu duk sanda kuka GA dama ku shirya ku ta dama ni ko a jikina ko kuma mutum ya bar industry din tuda ba da ita aka haifeshi ba

don haka mu zamu ciyar da harkar gaba insha Allah tunda ku kunsa Hassada da muna furci da gwara kan masoyanku kuje kuyi tayi don haka ni na dogara GA Allah shine gatana ba wani MUTUM BA 🙏🙏🙏Tallata wakar ka : Send Email Or Call