Music: Saniyo M Inuwa Ku MataSaniyo M Inuwa Ku Mata

MUSIC: Saniyo M Inuwa Ku Mata


Mata Gafa Naku Saniyo M Inuwa Ya Sake Danno Muku Da Wata Sabuwa Mai Suna - Ku Mata

Kadan Daga Baitukanta

-Maza Mata ni Saniyo na M Inuwa ne, nine na rero wake samaa

-Matakin kune zama gidajen Aure, duk tsananin wuya maza sa jure, gurgun doki an faɗan bai tsere, masunci ai dole ai mai kore.

-Isah buga ganga, ni zanja zuga, shifa rabon ka naka ne ko anki, tsoron Damisa karon ta da Zaki, ai dole ce ta zamma kanwar naki, shiru shiru wadansu suka ce kirki,

-Sai nai Sallama nake buga ƙyaure, Gamji juriya ruwa sai Ɓaure, mai hakuri ban so ace ka sare, burin ɗan Adam ace ya kere, ku taka sannu kallo sai idanu,

-Shimfidar fuska ta wuce ta barma, mai san Zuciya shi zai yi ladama, Kudi a Duniya sune sha nema, a kasa kar ku dinga tada husuma,

-In kaki ji ance ba kaki gani ba, mai nazari ba za yayo shirme ba, in mun yi laifuka musa ran tuba, duk dan kasuwa yana son riba, Ruwa ya sauka Gona ai shuka,

-Nayi uwar rago ake wa jaje, duk inda kuka jamu mu sai mun je, mai tafiya ai zai tsaya in yaje, mu zaku yo gani gurin in kunje,

-Ƴan yara yara gobe sune manya, shi kuma yayyafi ya kan hana shanya, batu na tausayi ku kalla Maraya, Isah Gombe ban kida na Garaya, Yara kuyi tafi, da jin tausan tsofi.

wadannan kadan kenan daga da ɗaɗaɗan bai tukun da wakar ta kunsa, masu dimbin daɗin sauraro tare da fadakarwa

Down-load HereDomin tallata Wakar ka Album ko Video, Aika mana da sako yanzu haka ta hanyar Email

This is an email link: Send Mail