Kannywood: Jaruma Abida Muhammed Zata Sake Yin Aure
Abida Mohammed zata sake yin aure

Kannywood: Abida Muhammed zata sake yin aure


Tsohuwar fitacciyar jarumar fina-finan hausa Abida Muhammed zata sake aure.
Za'a daura aurenta da Almustapha Abubakar ranar juma'a 26 ga wata a garin Kano dai dai karfe hudu na yamma.

Jarumar zata sake aure ne bayan mutuwar tsohon mijinta Hamza Rijiyar Zaki wanda ya rasu shekarun baya.

Abida Muhammad tana cikin Jaruman da suka taka muhimmiyar rawa wajen farfado da masana'antar fina-finan hausa kuma tauraronta ya haska kwarai da gaske.

A zamanin da tsohuwar jarumar take tashe tana sahun gaba cikin jerin matan da ake ji dasu a farfajiyar masana’antar shirya fina-finan Hausa.

Bayan auren ta da tsohon mijin ta marigayi Hamza Rijiyar Zaki aka daina jin duriarta a dandalin fim.

Tallata wakar ka : Send Email Or Call