Sababbin Jarumai 5 Dake Tashe Yanzu A Masana'antar Kannywood
Sababbin Jarumai 5 Dake Tashe Yanzu A Masana'antar Kannywood

Sababbin Jarumai 5 Dake Tashe Yanzu A Masana'antar Kannywood


Rubutawa : Faisal Abbas NG

Hakika Tauraron su na haskawa kuma da alama sun shirya damawa da sauran fitattun jarumai dake masana'antar Kannywoodwanda cikin su harda shahararren mawakin nan Umar M Shareef jarumi a Film din Mansoor

Gadai Jaruman Kamar Haka.

1= Maryam Yahya

Maryam Yahaya

Jaruma Maryam Yahya, jaruma a Film din Mansoor matashiyar jaruma ce wacce za'a iya cewa ta tsinci dami a kala a Film dinta na farko inda ta maye gurbin jarumar Film din a yayin da tayi jinkiri wurin isowa farfajiyar daukar shirin

Wanda hakan ya zame mata sila ta daukaka da, da kuma dumbin farin jini da tarin masoya ta yadda yanzu haka da yawa cikin masu shirya fina-finan hausa suke rige rige wurin sakata a Fina Finan su

2= Umar M Shareef

Umar M Shareef

Umar M Shareef Mawaki kuma Jarumi a masana’antar Kannywood

Mawaki Umar M Shareef Mawaki ne daya shahara kuma yayi fice a fagen rere wakokin Fina Finan Hausa kafin daga bisa yanzu ya fara fitowa a matsayin jarumi a Film
Hakika jarumin Mawakin ya taka muhimmiyar rawa tun a Film din sa na farko mai suna Mansoor,  wanda yaja hankalin miliyoyin al'umma, kuma hakika kwalliya ta biya kudin sabulu domin kuwa da yawa cikin al'umma sun yaba da irin jarumtar da jarumin ya nuna

Inda tun bayan haska Film din da akayi a gidajan "Senima" kafin a fitar dashi kasuwa wani kamfanin shirya fina-finan ya fara zawarcin jarumin domin saka shi a wani sabon Film dinsu mai suna "MARIYA"

3= Amal Umar

Amina Amal

Jaruma Amal Umar sabuwar jaruma ce dake tasowa wacce yanzu haka itama ke kan gaba wajan gogayya da manyan Jarumai a farfajiyar Kannywood

Sannan amiya ce, kuma kawa ga Jaruma maryam Yahaya domin kuwa jinin su yayi matukar haduwa

Daga cikin fina finan da jarumar tayi akwai. Rabu Da Maza, Duhun Kai, Larai Ko Jummai, da sauran su.

4= Rashida Labbo

Rashida Labbo

Jaruma Rashida Labbo tana daya daga cikin wadanda suka sami kyautar karramawa ta Mujallar People City award na wannan shekarar.

5= Garzali Miko

Garzali Miko

Jarumi Garzali Miko, Jarumin da duniya ke mararin gani, garzali miko matashin jarumi da yanzu haka tauraruwar sa ke kan gaba wurin haskawa a masana’antar Kannywood
Jarumin ya fara samun shahara ne da daukaka tun a lokacin da Video wata wakar Film ɗinsa mai suna Hasashe ta bayyana, tun bayan fito warsa a cikin wani Film wanda ya hada matasan jarumai da yawa mai suna "Gamu nan dai" Karkashin jagoran cin sarki Ali Nuhu

Hakika wakar sa ta Hasashe tayi matukar jan hankali matasa dama daukakin ma'abota kallon finafinan Hausa ciki harma da wasu manyan jarumai a masana’antar Kannywood

Kamar irin su Ali Nuhu da Kuma Adam A Zango, inda Zango ya jinjina masa

Wanda ya zuwa yanzu jarumin ya fito a Fina Finai da dama wadanda wasunsu sun fito wasunsu kuma basu fito ba inda yanzu haka kuma yake ci gaba da daukar wasu

Garzali Miko Mariya

Wannan hoton dake kasa daya ne daga cikin hotunan wani sabon shirin Film da jarumin ke dauka.

Tallata wakar ka : Send Email Or Call