Mawaki Classik Ya Lashe Kyautar Gwarzo Shekara Na Sarauniya Beauty Pargent
Mawaki Classiq Ya Lashe Kyautar Gwarzo Shekara Na Sarauniya Beauty Pargent

Mawaki Classik Ya Lashe Kyautar Gwarzo Shekara Na Sarauniya Beauty Pargent

Fitaccen mawakin hip-hop Buba Barnabas wanda aka fi sani da Classik a.k.a Captain sama a.k.a Arewa Mafia, ya yi nasarar lashe kambun kyautar Sarauniya Beauty Pargent wanda ake ba mawakan hip hop na Arewa da ‘yan wasan Hausa a duk shekarar.

An kaddamar da bikin ba da kyautar ne a Kaduna inda ya samu halartan manya baki daga sassa na duniya daban-daban, da kuma manya jaruman kannywood da mawakan Arewa kamar su:

Rahma Sadau da Umar M. Shareef da Aminu Shareef Momo da Adam Zango da Ado Gwanja da Sani Danja da Fati NIjar da MCTagwaye da Funky Malam da Funkiest da Morell da  Dj Abba da D Project da Stly-Plus da Dan Zaki da Penny, Abbas Sadik da dai sauran su.

Ya samu nasarar lashe kambun ne saboda wakokin da ya yi wannan shekarar da kuma irin karbuwar da ya samu a gurin al’umma mussamman ‘yan Arewa.

Classik ya bayyana farin cikinsa ga Allah, Kuma yana godiya ga Beauty Pargent da suka karrama shi, da kuma masoyansa da suka ba shi goyon baya, ya kuma kara da cewa “A rayuwarsa ba shi da wani abin alfahari da ya wuce masoya, domin kuwa ba don su ba da bai je ko’ina ba”, ya bayyana hakan ne a wata hirar da ya yi da wakilinmu UMAR MUHSIN CIROMA.

Matashin dan asalin garin Bauci, haifaffen garin Jos, ya kuma taso ne a jihar  Kano inda ya kammala karatun digree din sa a Bayero Unibersity da ke Kano, daga nan ne kuma ya koma Legas da zama don ci gaba da harkar waka.

Daya daga cikin  wakokinsa da suka yi tashe a shekarun baya, ita ce ta bidiyon “I Lobe U”. wanda ya yi tare da fitacciyar jarumar Kannywood wacce ta samu nasarar lashe gasar zama zakarar LEADERSHIP NEWSPAPER a wannan shekarar, Rahma Sadau.

Dik da ‘yan matsalolin da aka samu a wancan lokacin na sanadiyyar fitar da bidiyo “I Lobe U” ta hanyar bogi, hakan bai hana bidiyon samun karbu wa a idon mutane ba, domin kuwa har yanzu babu bidiyon hip hop da aka kalla a Intanet sama da “I Lobe U”.

Tallata wakar ka : Send Email Or Call