Fina-finan Hausa 5 mafiya shahara a shekarar 2017

Fina-finan Hausa 5 mafiya shahara a shekarar 2017

Fina-finan Hausa 5 mafiya shahara a shekarar 2017


Masana’antar shirya finafinai ta Kannywood na dada samun ci gaba a kullum musamman in aka yi la’akari da ingancin aiki da kwarewa da ake ta samu a masana’antar tun daga kan ‘yan wasa har zuwa masu bada umarni, masu shiryawa, masu daukar hoton bidiyo da dukkan bangarori da ma’aikatan shirya fim.


Kowane bangare da ke da hannu wajen shirya fim a Kannywood na kokarin ganin ya inganta yadda ya ke gudanar da aikinsa, dalilin da ya sanya jama’a suka dada karbar fim din Hausa a gida da waje

Finafinai da dama sun kayatar a shekarar nan mai karewa, mun yi nazari tare da gabatar da bincike, inda muka fitar da finafinai biyar da aka fi kalla a shekarar 2017

1. SAFARA

Fim din Safara fim ne da ya yi nazari akan dabi’ar nan ta safarar mutane a arewacin Nijeriya musamman mata da kananan yara.

Fim din na dauke da dingima-dingiman jarumai kamarsu Ali Nuhu, Abba El-Mustapha, Aminu Sharif Momo, Jamila Nagudu, Aina’u Ade, Ladidi Fagge da sauransu

2. MANSOOR

Mansoor na daya daga cikin finafinan shekarar 2017 da aka fi tattaunawa akansa tun gabanin fitowarsa. Hakan ya sanya ‘yan kallo tsumayin fitowar fim musamman yadda mai fim din (Ali Nuhu) ya tallata fim din

Fim din Mansoor ya faro da yadda wasu maketata ‘yan makaranta ske cin zalin wani salihin dalibi, zuwa soyayya tsakanin salihin dalibin da wata yarinya ‘yar makarantar zuwa buduwar sirrin MANSOOR din wanda shi ne ya yi warwara akan labarin fim din

Fim din Mansoor na dauke da jarumai kamarsu Ali Nuhu,Abba El-mustapha, Baballe Hayatu, Umar M. Shariff da Maryam Yahaya
3. RARIYA

Fim din Rariya labari ne akan wasu ‘yan mata daliban jami’a tare da bayyana yadda wasu ‘yan mata ke amfani da damar ‘yancin da suke samu na zaman kansu a jami’a su sheke aya. Fim din ya kuma nuna yadda wasu ‘yan mata ke zubar da tarbiyyar da iyayensu suka basu da zarar sun shiga jami’a

Fim din na dauke da manyan jarumai kamarsu Ali Nuhu, Rahama Sadau, Hafsat Idris, Maryam Booth, Fati Washa, Sadik Sani Sanik da dai sauransu

4. AUREN MANGA

Fim din Auren Manga fim ne na barkwanci da zai yi tasiri wajen yaye damuwa a zuciyoyin al’ummar Hausa masoya finafinan Kannywood.

Fim dinna dauke da jaruma Hadiza Gabon, Sule Yahaya Bosho da Falalu Dorayi

5. KALAN DANGI

Kalan Dangi Labari ne na soyayya, karya da shahara…

Jarumai sun hada da: Ali Nuhu, Aminu shariff momoh, Fati Washa da Sadik Sani SadikTallata wakar ka : Send Email Or Call