An Sako Jarumi Alameen Buhari Bayan Anyi Garkuwa Dashi

Anyi Garkuwa da jarumi Alameen Buhari

An Sako Jarumi Al'ameen Buhari Bayan Anyi Garkuwa Dashi


Labarin da ya riske mu a ya tabbatar da cewa an saki Jarumin Finafinan Hausa `Al'amin Buhari` wanda wadansu masu garkuwa da mutane wadanda ba a san ko su wanene ba suka sace shi a hanyar Abuja a daren Ranar Lahadin da ta gabata.

Yanzu haka dai masu garkuwan da mutanen sun saki Jarumin kuma yana Abuja cikin koshin Lafiya.

Manema Labarai sun samu damar magana da jarumin a wayar wani abokin sa inda ya tabbatar da cewa yana nan da rai kuma zai Koma wurin iyalin shi da ke a garin Jos in-sha Allah.

Tun farkon Ranar talata ne labari ya bazu cewa an sace Jarumin kuma ba'asan inda yake ba, Inda daga baya kuma aka samu kira akan cewa sai an bada wasu kudade sannan a sakeshi.

Kawo yanzu dai ba wani tabbacin ko an biya wasu kudade ne kafin a sake Jarumin. Muna fatan Allah ya kiyaye gaba.Tallata wakar ka : Send Email Or Call