Ko Yanzu Na Samu Miji Da Gudu Zan Yi Aure - Rashida Mai Sa'a
Ko Yanzu Na Samu Miji Da Gudu Zan Yi Aure Rashida Mai Saa

Ko Yanzu Na Samu Miji Da Gudu Zan Yi Aure - Rashida Mai Sa'a


Fitacciyar tsohuwar jarumar nan ta fina-finan Hausa a masana'antar Kannywood kuma 'yar siyasa mai suna Rashida Adamu mai sa'a ta bayyana cewa suna matukar shan wahala yanzu wajen samun mazajen aure.

Jarumar dai ta bayyana hakan ne a 'yan kwanakin nan kamar dai yadda Mjallar fim ta ruwaito, ta bayyana cewa a duk lokacin da ta samu mijin aure, to fa da gudu zata aure shi.

Jarumar ta kara da cewa: "Samun Mazan Ne Da Wahala, Amma Ko Yanzu Na Samu Miji Da Gudu Zan Yi Aure".

Mai karatu dai zai iya tuna cewa jarumar tuni ta dauke kafar ta daga fitowa a matsayin jaruma a cikin fina-finai sannan kuma ta tsunduma cikin harkokin siyasa inda daga baya ma har ta samu mukamin mai bayar da shawara ga Gwamnan jihar ta Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje.

Tallata wakar ka : Send Email Or Call