Shin Da Gaske Ne Ali Nuhu Ya Auri Jaruma Hadiza Gabon

Shin Da Gaske Ne Ali Nuhu Ya Auri Jaruma Hadiza Gabon

Shine Da Gaske Ne Ali Nuhu Ya Auri Jaruma Hadiza Gabon ?


Shahararren jarumin nan na Kannywood, Ali Nuhu ya karyata rade-radin dake yawo cewa ya auri jarumar Kannywood Hadiza Gabon cikin sirri.

Jarumin wanda aka fi sani da sarki mai Kannywood ya bayyana hakan ne a wani hira da yayi da jaridar Daily Trust.

Kwanan nan wani hoton Ali Nuhu da Gabon ya yi fice a shafukan zumunta inda ake ce jaruman biyu sunyi aure a Kano.

Ali Nuhu wanda ya kasance shugaban kamfanin FKD Film Production ya bayyana cewa wasu mutane na nan wanda burinsu shine yada jita-jita ba tare da tunanin abunda ka iya zuwa ya dawo ba.

Ya kara da cewa wannan hoto da ya haifar da jita-jita shirin wani fim ne mai suna ‘Akushi’ inda jarumar ta fito a matsayin matarsa.Tallata wakar ka : Send Email Or Call