Dalilin Daya Sa Bana Sanya Kananan Kaya - Aisha Aliyu Tsamiya
Labarin Jaruma Aisha Aliyu Tsamiya

Dalilin Daya Sa Bana Sanya Kananan Kaya - Aisha Aliyu Tsamiya


Fitacciyar jarumar nan ta wasan fina-finan Hausa a masana'antar Kannywood kuma 'yar asalin jihar Kano mai suna A'isha Aliyu da ake yi wa lakani da A'isha Tsamiya ta fito ta bayyanawa duniya babban dalilin da ya sanya ita bata saka kananan kaya kamar sauran wasu jaruman.

Jarumar dai ta bayyana cewa ita ba ta sa kananan kaya ne musamman saboda dalilin cewa ba sa yi mata kyau idan ta sa su don kuma ta dan gwada a lokutan baya.

Kamar yadda majiyar mu dai ta samu cewa wasu da daga cikin jarumai mata a masana'antar fim din kan sanya kananan kaya a yanayin rayuwar su ta yau-da-kullum ko kuma ma a cikin fim amma ba'a taba ganin ita A'isha Tsamiya din ba da su.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa a kwanan baya ma dai mun kawo maku labarin yadda wata kungiya a arewacin kasar nan tayi kira ga matan yankin da suyi koyi da dabi'un jarumar fim din Rahma Sadau wanda kuma hakan ya jawo cece-kuce a tsakanin mata da maza a yankin inda suke ganin hakan bai dace ba.

Tallata wakar ka : Send Email Or Call