Takai Taccen Tarihin Jarumi Abdul M Shareef

Tarihin Abdul M Sharif

Takai Taccen Tarihin Jarumi Abdul M Shareef


Daga  Umar Muhsin Ciroma, Kaduna

Tun lokacin da ya fito a cikin fim ɗin Jinin Jikina, jarumi Abdul M. Shareef ya fara haskawa a duniyar finafinan Hausa.

Abdul M. Shareef yana cikin ƙalilan matasa a Kannywood da Allah ya horewa abubuwa da dama. Baya ga haka, ƙwararren jarumi ne da kowa ya gamsu da ƙwarewarsa.

Abdul M. Shariff yaya ne ga sanannan mawakin Hausa Umar M. Shariff, kuma ƙani a wurin fittaccen daraktan Kannywood Mustapha M. Shariff, har ila yau, yana da kyakkyawar dangantaka da shahararren jarumi Ali Nuhu, (Sarkin Kannywood) wanda kusan za a ce shi ya ba shi dama domin ya nuna ma duniya fasaharsa.

Haifaffen garin Kaduna nane a Unguwar Rigasa Ya taso, inda ya fara karatunsa na Firamari a (Amana International School) har zuwa aji uku, kana ya kammala a (Bakoma Ulumudden Nasaasa Primary School) ya kamala makarantar sakandiren Gwamnati da ke Rigasa a cikin Jihar Kaduna. Daga nan ya shiga makarantar koyan Kwamfuyuta (RCSDC), bayan nan sai ya tsunduma harkan fim.

Daga cikin abubuwan da masu sha’awar kallon finafinan Hausa ke so akwai ƙwarewar rawa, Abdul na sahun gaba cikin jerin jaruman da suka ƙware a wannan fanni. Yana ƙoƙari ƙwarai gurin ganin ya motsa jiki don burge masoyansa.
Shariff ya fara harkar fim da daɗewa, yana bayyana ne a bayan fage, daga bisani ne ya fara shiryawa da tsara finafinai. Sannu a hankali ya fara fitowa cikin finafinai a matsayin jarumi. ‘Yar Agadaz na ɗaya daga cikin finafinansa ɗinsa na farko. Zuwa yanzu ya fitowa a finafinai masu yawan gaske Tuni ya sanya kansa jerin jaruman da duniyar Kannywood ke alfahari da su.

Aƙalla yanzu ya kai shekaru goma sha ɗaya da fara harkar fim, amma da fara bayyanarsa yau shekara Biyar kenan. Kusan duk wasu abubuwa na ci gaban masana’antar a gabansa suka faru. Mafarkinsa na zama cikakken jarumi a Kannywood ta ja shi ga harka finafinai inda ya fara tun daga tushe har kawo matsayin da ya tsinci kansa na shahararren jarumi a Kannywood.

Ya fara aiki ne a kamfanin Dorayi Production, ya yi finafinai da dama amma kuma fim ɗinsa da ya fara haska shi a idon duniya shi ne Jinin Jikina.

Jinin Jikina fim ne wanda aka yi a shekara ta 2014 shaharerran kamfanin Shareef Studio ne suka ɗauki nauyin shiryawa, kuma Sarkin Kannywood, Ali Nuhu ya rubuta labarin ya kuma bada umarni, kana shaharerren mawaƙin Umar M. Shariff ya rera waƙoƙin da suka taimaka gurin ɗaga darajar fim ɗin.

Shareef Studio sun taimaka ƙwarai wajen ganin sun haska matashin jarumin da za a iya cewa ya shigo masana’antar da ƙafar dama. Daga cikin manyan jaruman da suka fito a wannan fim din ya haɗa da babban Jarumi Ali Nuhu, Rahama Sadau, Rabi’u Rikadawa da dai sauransu.

Abdul ya taka muhimmiyar rawa a cikin Fim ɗin, wanda haka ya sa ya haskaka tauraruwarsa a idon duniya, ganin ƙwazon da Abdul ya nuna a cikin shirin Jinin Jiki na, ya janyo hankalin Furodusoshi da Daraktoci suka fara ribibinsa.


Ali Nuhu, ya taimaka ƙwarai wajen ganin ya ƙara zaƙulo basirar da Allah ya yi wa jarumi Abdul tare da nunawa duniya irin fasaharsa. Ya kuma tabbatar ma duniya cewa Abdul mutun ne mai son mutane, yana mai da hankali ƙwarai idan har aka ce an zo bakin aiki, ba ya wasa da duk abun da aka saka shi. A yanzu haka duk wani matakin da ake buƙatar jarumi ya kai, to fa Abdul M. Shariff ya ɗauki hanyar shiga wannan wajen.

Kowane jarumi burinsa ya samu ɗimbin masoya domin a riƙa gayyatarsa wurare don nishaɗantar da mutane, Abdul ya hau kan wannan ƙadami na zama shahararre.

Kwanan nan akwai sababbin finafinai guda uku nasa da jama’a suke ɗaukin fitowarsu Ja Ni Mu Je, Burina da kuma Yaƙi A So.

Jani Mu Je fim ne wanda shi ma Shareef Studio ne suka ɗauki nauyin shirya shi, kuma Mustapha M Shariff ya ba da umarni. A cikin fin ɗin akwai fitattaun jaruma da suka haɗa da Shu’aibu Lawal, Tijjani Asase, Nafisa Abdullahi da dai sauransu,

Bidiyon waƙar Zaara da take cikin fim ɗin tana ɗaya daga cikin waƙoƙin da suka shahara a shekara ta dubu da sha bakwai, wanda tun kafin a saki faifansa mutane sun gama karɓar sabon tsarin da aka zo masu da shi. A YouTube kaɗai, Yana ɗaya daga cikin waƙar Hausa da aka kalla a shekarar 2017, domin zuwa yanzu aƙalla mutum dubu ɗari uku da ashirin da biyar (325,000) ne suka kalle ta. Kaɗan ne daga cikin waƙoƙin manyan jarumai suka samu wannan tagomashin.

Burina fim ne wanda shi kuma NICE ENTERTAINMENT NIGERIA LTD. ne shirya, har ila yau Mustapha M Shariff ya ba da umarni, Musa Namalam Bole ne ya rubuta kuma ya shirya fim ɗin, Ali Nuhu ne ya bada umarni. A cikin fin din akwai fitattaun jarumai irin su Ali Nuhu Shu’aibu Lawal, Rabi’u Rikadawa Ladidi Fagge, Nafisa Abdullahi sai kuma shi Abdul.

Babban abin dubawa a nan shi ne, a wannan shekarar da muke ciki, manya-manyan jarumai sun saki finafinai waɗanda suka yi tashe matuƙa, amma hakan bai hana fim din da ɗan wasan Abdul ya haska ba, domin shi ma duniya yanzu ta san shi.

Ya fuskanci ƙalubale da dama, amma hakan bai sa shi ya karaya ba, ko jin ba zai kai labari ba, ya yi imani da cewar duk abun da ka jajirce a kai to Allah zai taimake ka.

Yana mai cewa, “ƙalubale a harkar rayuwa duk abinda ɗan’dam ke yi wani lokaci a samu farin ciki wani lokaci kuwa a sami akasin haka.

Kaɗan daga cikin finafinan da ya fito a ciki: Makashinka, Bazan Bar Ki Ba, Ka So A So Ka, Gangar Jiki, Amira, Wata Uwa, Lamina, Biki Buduri, Ja Ni Mu Je, Jinin Jikina, , Burina, ‘Yar Agadaz da dai sauransu.Tallata wakar ka : Send Email Or Call