Jaruma Umma Shehu Ta Kunyata A Idon Duniya Arewa24

Jaruma Umma Shehu Ta Kunyata A Idon Duniya
Umma Interview

Fitacciyar jarumar nan ta fina-finan Hausa a masana'antar Kannywood ta kunyata a idon duniya a cikin wani shiri na Kundin Kannywood na gidan talabijin din Arewa 24 da yakan gayyato jarumai domin tattaunawa da su.

A cikin firar dai da Jarumi Aminu Shariff wanda aka fi sani da Momo da kuma ke zaman jagoran shirin yayi wa jaruma Umma Shehu tambaya ne game da bangaren musulunci inda ya tambayi jarumar ko wacece ta shayar da manzon Allah.

Jaruma Umma Shehu Ta Kunyata A Idon Duniya
Really Umma Shehu 

Majiyar mu ta samu kuma dai cewa jin wannan tambayar ne ke da wuya sai jarumar hankalin ta ya tashi inda ta nuna rashin jin dadin ta game da lamarin har ta tambaye shi yaya zai yi mata haka duk da dai cikin dariya da raha.

Haka ma dai a cigaba da tsokacin da mutane ke ta yi game da lamarin, da dama sun soki Aminu Momo din da yi mata tambayoyin da ba su da alaka da wannan shiri yayin da kuma wasu ke ganin jarumar ta yi abin kunya na rashin amsa wannan tambaya.Tallata wakar ka : Send Email Or Call