Abubuwa 5 Dasu Kamata Ku Sani Game Da Marigayi Lil Ameer.
Tarihin Lil AmeerHakika masana'antar nishatarwa ta Arewa tayi babban rashi da rasuwar dan matashi mawakin hausa hip hop, amma indai ajalin mutum ya kai babu wanda zai iya kubutar dashi.

Ameer Isa Hassan ya rasu ranar 14 ga watan Satumba a garin Kano sanadiyar hatsarin mota. Anyi jana'izar shi ranar juma'a a layin massalacin juma'a na tarauni.
ga wandada basu san labarin wannan matashin ga abubuwa 5 da ya kamata ku sani;

1. Haifafan Dan jihar kano ne

An haifi marigayi Ameer a cikin 2003 a jihar Kano

2. Har zuwa lokacin rasuwar sa mawakin yana koyan darasi a makaranta

Duk da kasancewar shi wanda ya fara shahara a harkar wakoki marigayi bai bari harkar ta dauki hankalin shi wajen koyan darasi. ya kan tafi makarantar boko kuma idan ya tashi yaje na islamiyya. sai karshen mako yake samun damar yin aikin waka. babban burin marigayi shine in ya gama karatu ya zama matukin jirgin sama.
Lil Ameer Isa Hassan.
3. Iyayen sa sun mara mai baya

hakika iyayen suka bashi damar fara waka kuma uwar take taimaka masa wajen rubuta wakokin.

Ameer Da Mahafiyarsa
Ameer ya canza makarantu domin masoyan sa sukan tunkare shi idan yana koyan darasi.

4. Ya fara waka tun yana jjs 1 na makarantar sekandare

matashin ya fara waka ne domin tun yana dan karami yake muradin waka. ya fara waka ne domin ya nuna ma duniya cewa matasa daga yankin arewaci kasar nan na iya rera waka kuma su yi nasara.

5. Yayi wakoki da dama kuma yayi wasa tare da sauran shaharren mawaka


cikin wakokin da marigayi yayi akwai "boss", "champion", "ilimin boko da addinin musulunci", "dance for me" da dai sauran su.

A Film Show A Kano
Matashin wadda ake wa lakabi "karaminsu babbansu" yayi waka tare da shaharraru da dama kuma yayi wassanni da dama a wurare daban-daban#

Lil Ameer Da Ado Gwanja 
Ameer Tare Da M Sharif
Ameer Tare Da ClassiQ
Ameer Tare Da Maryam A Baba. 

Ya Allah Kaji kan Ameer Isa Hassan Dan Batta Kakai Haske Kabarin Sa Ameen.

Tallata wakar ka : Send Email Or Call