Zan Hadawa Duk Wanda Zai Aureni Kayan Lefe - Jaruma Hauwa Waraka

Hauwa Waraka

Zan Hadawa Duk Wanda Zai Aureni Kayan Lefe Inji Jaruma Hauwa Waraka.

Marubuci : Faisal Abbas NG

Jarumar ta fadi hakan ne cikin wata fira da tayi da shafin BBC Hausa.

Cikin raha Jarumar ta zolayi ma'aikacin gidan jaridar Bbc Hausa daya tambaye ta shin Ko yaushe zatayi Aure.

Jarumar tace hakika tana son yin Aure, kuma ta kara da cewa “kai ma wakilin BBC Idan kana sona ka Fito. Wallahi Aure na bazaiyi tsada Ba. Kai, ni zanma hada ma kayan Lefe akwati shida Idan kana so.

Koda yake nasan tsoron matarka kake yi kada kaje gida taki bude maka kofa.... (Dariya) Hhhhh

Sannan Jarumar ta kara da cewa dalilin da yasa take fitowa a mutuniyar banza a film shine domin ta fadakar da al'umma game da irin Illolin dake tattare da hakan.

Tace ban taba karuwanci ba, kuma bata taba hulda da karuwai ba, Amma Idan tana tana taka rawa a film a matsayin karuwa, kai kace ni magajiya ce.

Sannan ta kara da cewa macen da zata fito a film a matsayin karuwa Ko 'yar shaye shaye, to bai kamata a ganta tas ko a ganta da hijabi ba.

Shi yasa Idan na fito a film zakaga Ina keta rashin mutumci, kuma hakan shine ya dace.

Amma kuma sau tari nasha zuwa unguwa mutane suna cewa, wacce irin kwaya ko wiwi zasu kawo mun nasha.

Basu san cewa ban taba shan kayan maye ba; wallahi ko taba ban taba sha Ba, Duk abunda suke gani a film ne kawai.

ZARGIN LUWADI DA MADIGO.

Da aka tambayi Jarumar kuwa game da zargin da ake yiwa' yan hausa film dayin Luwadi da Madigo.

Jarumar tace Gaskiya akwai bara-gurbi sosai a cikin su, kamar yadda akwai su ako ina har cikin malamai ma, Domin haka bai kamata mutane su rinka yi musu kudin goro Ba.

Sannan ta nemi mutane su rinka yiwa 'Yan Film Uzuri sabo da suma mutane ne kamar kowa.

® www.HausaMp3.Com.ng
Tallata wakar ka : Send Email Or Call