Takai Taccen Tarihin Jarumi Garzali Miko

Takai Taccen Tarihin Garzali Miko

Takai Taccen Tarihin Jarumi Garzali Miko


An Haifeshi Ne A Shakarar 1993 A Garin Kano Dake Arewacin Nigeria.

Yayi Karatun Primary Din Sane A (Gyadi-Gyadi Special Primary) Daga Nan Kuma Sai Ya Wuce Makarantar Secondary Ta Horizon Duk A Cikin Garin Kano.

A halin yanzu kuma yana karatun difloma kan sha’anin wasannin kwaikwayo a jami’ar Maitama Sule.

Yana da kyakkyawar dangantaka da jarumi Ali Nuhu, (Sarkin kannywood) wanda kusan za a ce shi ya raine shi har zuwa lokacin da ya felle domin kokarin kafa kansa. Garzali Miko fara harkar fim a matsayin mai bada hasken wuta, daga bisani ne ya fara shiryawa da tsara finafina.

Yanzu haka yana cikin manyan furodusoshi da ake ji da su a masana’antar finafinan Hausa. Ya shirya finafinai da yawa, yayin da wasu ma shi ya fito a matsayin jarumi. Ya fara harkar fim ne tun yana yaro karami bai wuce shekara goma ba, kusan duk wasu abubuwa na ci gaban masana’anyar a gabansa suka faru.
Mafarkinsa na zama cikakken Jarumi a Kannywood ta ja shi ga harka finafinai inda ya fara tun daga tushe har kawo matsayin da ya tsinci kansa na shahararren jarumi a Kannywood, ya fara aiki ne a kamfanin Rana Film Production, ya yi finafinai da dama amma kuma fim dinsa da ya fara haska shi a idon duniya shi ne Gamu Nan Dai.

Ku Karanta Wannan.  Gamu Nan Dai fim ne wanda shaharerran kamfanin FKD suka dauki nauyin shiryawa, kuma gogarman Kannywood, Ali Nuhu ya bada umarni. FKD sun taimaka kwarai wajen ganin sun haska matasa hudu daga ciki har da shi Garzali Miko. Matasan da suka fito a wannan fim sun hada da Ramadan Booth, Nuhu Abdullahi, Shamsu Dan Iya, Abdul M Shareef, sai kuma jagoran shirin Ali Nuhu.

Ganin kwazon da Garzali ya nuna a cikin shirin Gamu Nan Dai, ya janyo hankalin daraktoci suka fara rige-rigen aiki da shi. Darakta Sunusi Oscar 442 ya taimaka kwarai wajen ganin ya kara zakulo basirar da Allah ya yi jarumi Garzali tare da nunawa duniya irin fasaharsa.

Ya kuma tabbatar ma duniya cewa Garzali mutun ne mai son mutane, yana mai da hankali kwarai idan har aka ce an zo bakin aiki, ba ya wasa da duk abun da aka saka shi. A yanzu haka duk wani matakin da ake bukatan jarumi ya kai, to fa Garzali Miko ya dauki hanyar karasa wannan wajen. Kowane jarumi burinsa ya samu dimbin masoya domin a rika gayyatarsa wurare don nishadantar da mutane, tunin Garzali ya hau kan wannan kadami na zama shahararre.

Babbar Sallah ta gabata, kusan duk gidajen wasannin Arewacin Nijeriya, wakokin Garzali ake sanyawa domin a cashe, musamman Hasashe da Arashi. Wakokin Hasashe da Arashi sun tasiri matuka a tarihin Kannywood, domin ba a taba samun matashin jarumi da ya fito da wakoki wadanda suka karbu a wajen mutane cikin kankanin lokacin kamar Garzali ba.

Babban abin dubawa a nan shi ne, a wannan shekarar da muke ciki, manya-manyan jarumi sun saki finafinai wadanda wakokinsu suka yi tashe matuka, amma hakan bai hana wakokin da jarumi Garzali ya fito bankawa wadanda jaruman domin shi ma duniya ta san shi ba. Bidiyon wakar Hasashe yana daya daga cikin wakokin da suka shahara a shekara ta dubu da sha bakwai, wanda tun kafin a saki faifansa mutane sun gama karbar sabon tsarin da aka zo masu da shi.

A YouTube kadai, babu wata wakar Hausa da aka kalla kamar ta Hasashe a shekarar 2017, domin zuwa yanzu akalla mutum dubu dari biyar (500,000) ne suka kale ta. Ko wakokin manyan jarumai ba su samu wannan tagomashi ba. Ya fuskanci kalubale da dama, amma hakan bai sa shi ya karaya, ko jin ba zai kai labari ba, ya yi imani da cewar duk abun da ka jajirce a kai to Allah zai taimake ka. A wata hira da aka yi da shi, Garzali ya ce sha’awa ce ta ja shi ga harka finafinai inda ya fara tun daga tushe har kawo matsayin da ya tsinci kansa na jarumi a Kannywood.

Yana mai cewa, “kalubale a harkar rayuwa duk abinda dan’dam keyi wani lokaci a samu farin ciki wani lokaci kuwa a sami akasin haka. Kadan daga cikin finafinan da ya fito a ciki: Hadari, Ameerah, Zee Zee, Guguwar So, Makaryaci, Wata Dukiya, Dan Masani, Idan Ana Dara, Rai Da Rai, Bakin Kishi da sauran su.Tallata wakar ka : Send Email Or Call