Rahama Sadau Ta Lashe Kambu A Masana’antar Nollywood

Rahama Sadau Nollywood

Jaruma Rahama Sadau Ta Lashe Kambun BON A Masana’antar Nollywood.

Farawa da iyawa fitacciyar jarumar nan ta wasannin fina-finan Hausa na masana'antar Kannywood da a kwanan baya aka dakatar da ita da kuma ta shilla zuwa masana'antar fina-finan kudancin kasar nan na Nollywood tuni har ta fara lashe kyauta.

Mun samu dai cewa jarumar yanzu haka an lissafa ta a matsayin jarumar da ta lashe kyautar nan ta BON a rukunin yan wasa sabbin jini tare da wani jarumin kuma Namiji mai suna Gbenro.

Majiyarmu dai ta samu cewa jarumar ta sanar wa da duniya wannan nasarar da ta samu ne a shafin ta na Instagram inda ta bayyana cewa tana yiwa dukkan magoya baya da kuma masoyanta jinjinar ban girma.

A wani labarin kuma fitacciyar jarumar nan ta wasan Hausa a masana'antar Kannywood mai suna Hadiza Gabon ta fara fitowa a cikin fina-finan turanci na kudancin kasar nan watau Nollywood.Tallata wakar ka : Send Email Or Call