Nafisa Abdullahi Ta Zama Jakadiyar, Jaridar Leadership Hausa
Nafisa Abdullahi Jakadiyar Leadership

Nafisa Abdullahi Ta Zama Jakadiyar Gidan Jaridar Leadership A Yau.

Dag Sharfuddeen Baba, Kano, Najeriya.

A Larabar data gaba rukunin kamfanin dake buga Jaridun Leadership A Yau suka kammala shirye-shirye tsakanin kamafanin da fitacciyar Jarumar Nafisa Abdullahi wacce tayi suna wajen fita a matsayin mai haƙuri a fina-finan Hausa, inda ta zama Jakadiyar Leadership A Yau.

Bayan ƙulla wannan yarjejeniya Nafisa Abdullahi ta bayyana cewa, da farko dai ina miƙa godiya ta ga kamfanin Leadership A Yau, na yi matuƙar farin cikin kasancewa ni ce Jakadiyar Leadership A Yau ta farko. Yadda aka ɗauke ni da muhimmanci ne ya sa har ake so a mayar da ni Jakadiyar Jaridar Leadership A Yau.

Nafisa Abdullahi Leadership hausa

Nafisa A lokacin da aka kaddamar da ita a matsayin Jakadiyar Leardership A Yau.

Duk da tarin Jaruman da suke Nijeriya, an ɗauke ni, ni ce ta farko wanda aka ba ta wannan babban matsayi.

Don haka ina matuƙar farin ciki. Ta ci gaba da bayyana cewa, lalle zan bada ƙarfin gwiwa don in ga wannan alaƙa tamu ta ɗore fiye da yadda muke tunani za mu samu.

Jaruma Nafisa Abdullahi ba ta kammala jawabinta ba sai da yi kira ga al’umma, tace ina kira ga jama’ar gida Nijeriya dama ƙasashen waje, su rinƙa karanta Jaridar Leadership A Yau , domin za su rinƙa ganin abubuwa daban –daban waɗanda za su ilimantar, faɗakarwa da kuma nishaɗantar da su.

Tallata wakar ka : Send Email Or Call