Dalilin Da Yasa Naki Fitowa A Film Din Madigo A Nollywood 一 Rahama Sadau
Dalilin Da Yasa Naki Fitowa A Film Din Madigo A Nollywood Rahama Sadau

Dalilin Da Yasa Naki Fitowa A Film Din Madigo A Nollywood 一 Rahama Sadau.

An so in fito a yar madigo a wani fim din kudu amma naki amincewa”, inji Rahma Sadau Shahararriyar jarumar ‘yar fina-finan nan na Kannywood wacce, Rahama Sadau, wacce aka kora daga masana’antar Kannywood.

A wani fira da jarumar tayi da kafafen yada labarai na THE GUARDIAN, tauraruwa Rahama ta bayyana cewa an so ta fito a wani fim din ta na fina-finan kudu a matsayin yar madigo amma sai ta ki yadda saboda la’akari da daga inda ta fito watau arewa.

NAIJ.com kuma dai ta samu cewa da take tsokaci game da korar ta da kungiyar fina-finai tayi, Rahma Sadau tace ita wannan korar ma gaba ta kaita don kuwa yanzu idon ta ya kara budewa kuma ta kara samun wasu damammaki na gudanar da sana’arta a dukkan fadin duniya.

Haka nan kuma jarumar ta bayyana rungumar da tayiwa mawaki ClassiQ da tayi sanadiyyar korar tata a matsayin bangaren aikin ta da bai kamata a tsangwameta ba game da hakan.

Daga karshe ne kuma sai jarumar ta kara jawo hankalin mutane da cewa shifa tsoron Allah a zuciya yake don haka ba dai dai bane ba a rika yi mata kallon ‘yar iska don kawai tana sana’ar ta.

Tallata wakar ka : Send Email Or Call