Allah Bai Wajabta Mun Yin Aure Ba - Inji Ummi Zee Zee

Ummi Zee Zee

Allah Bai Wajabta Mun Yin Aure Ba Inji Jaruma Ummi Zee Zee.

Shahararriyar tsohuwar jaruma a wasan fina-finan Hausa mai suna Ummee Zee Zee ta fito ta fadawa duniya cewa Allah fa bai wajabta aure ba akan dukkan mutane don haka a shafa mata lafiya.

Kamar yadda muka samu daga majiyar mu, jarumar ya yi wannan kalamin ne kusan a matsayin raddi ga al'umma mutane da ke ta caccakar ta da kuma ire-iren ta da cewa sun ki suyi aure duk kuwa da cewa shekarun su sun ja.

Kamar Yadda A Kwanakin Baya Wata tsohuwar jarumar a masana'antar fina-finan Hausa Fati Muhammad ta fito ta bayyana babbar nadamar ta a rayuwa a matsayin auren dan fim Sani Musa Mai iska da tayi a shekarun baya.

Su dai jaruman fina-finan Hausa musamman ma dai mata a cikin su na fuskantar matukar matsin lamba daga al'ummar Hausa inda kuma a lokuta da dama akan zarge su da bata tarbiyyar jama'a.

Mun Cofo Daga Shafin :- Hausa.Naij.ComTallata wakar ka : Send Email Or Call