Kadan Daga Cikin Kyawawan Halayan Jaruma Hadiza Gabon

Kadan Daga Cikin Kyakykyawan Halayan Jaruma Hadiza Gabon

Kadan Daga Cikin Kyawawan Halayan Jaruma Hadiza Gabon.

Hadiza ko kuma Dijatou Aliyu wadda aka fi sani da Hadiza Gabon, tana daya daga cikin jarumai mata da suka shahara a farfajiyar finafinan Hausa.

Hadiza ta yi matukar kwarewa a duk wani matsayin da za a ba ta a fim, wanda hakan ya sa har yau ake damawa da ita a masana’antar, domin ba kowace jaruma ba ce za ta iya hawa irin matsayin da jarumar ke hawa a finafinai.

Kyakkyawar jarumar ta kuma kasance mai yawan masoya daga cikin jaruman fim, har ta kai ga ta samu daukakar da ita kanta ba ta taba zaton samu ba.

Allah ya azurta jarumar da kyawawan dabi’u na taimako, tausayi da jin kan mutane, musamman gajiyayyu, marasa karfi da kuma marayu.

Akwai lokacin da labarin wata nakasashiyar yarinya mai suna Rahama Haruna wacce ake dauka a cikin roba ana bara da ita a jihar Kano, lokacin da Hadiza ta ji labarin wannan yarinya sai ta tausaya sosai harma ta ziyarci yarinyar inda ta tallafa mata da kudade da kayayyakin abinci.

Hadiza Gabon Tare Da Rahama Haruna


Sannan kwanakin baya Hadiza ta ziyarci sansanin yan gudun hijira inda su ma tayi masu alkhairi mara misali, domin ta tallafa masu da kayan abinci, kamar yadda muka sani cewa yan gudun hijira sunyi fama da lalurar yunwa.

Hadiza Gabon A Sansanin Hijira


Bayan da Jaruma Hadiza Gabon takai ziyara sansanin 'yan gudun hijira wani abu, kuma da zai baka mamaki shine !

A lokacin da jaruma Hadiza za ta yi bikin zagayowar ranar haihuwarta, maimakon ta tara jama’ar da ba su dace ba a yi ta sharholiya, sai ta tattara kayayyakin bikin nata ta je gidan marayu, inda ta dauke su a matsayin wadanda za su taya ta bikin.

Hadiza ta yanka kek din bikin ranar haihuwarta ta tare da marayun kuma ta ci ta sha tare da marayun, domin a cewarta yin hakan wata hanya ce ta farantawa marayun rai, tare kuma da debe musu kewa, wanda bai kamata a ce ana mayar da su saniyar ware ba a al’amuran farin ciki dake gudana a kasar nan.

Hadiza Gabon Happy Birthday


Wannan ba shi ne karo na farko da Hadiza ta kai ziyara gidan marayu ba, domin aikinta ne ziyara gidan marayun inda take raba musu kayan abinci da kayan sawa.

Yara 'Yan Makaranta


Haka a bangaran Tai makowa yara 'yan makaranta harma da Almajirai Jarumar ba' a barta a baya ba, don kuwa ko cikin wannan watan da muke ciki sai da Jarumar ta rarraba kayan abinci ga wasu makarantun allo a jahar Kano.

Wadan nan sune kadan daga cikin kyawawan aiyukan alkhairin da Jarumar wasan Fina Finan Hausa Na Kannywood Hadiza Gabon take aikatawa ga al'umma marasa galihu a Nigeria.

Domin Haka A Mahadin Dukkan Daukakin Ma'ikatan Wannan Shafi Tare Da Dukkan Masoya Muna Yi Mata Fatan Alkhairi, Da Kuma Addu'ar Allah Ya Kareta Ya Kuma Kara Mata Daukaka Mafi Girman Daukaka A Cikin Rayuwarta Ta Duniya, Sannan A Lahira Ya Saka Mata Da Gidan Aljannah Madaukakiya Ameen.
Tallata wakar ka : Send Email Or Call