Jamilu Dakan Ɗaka Ya Baje Wasu Sirrin Dake Kamfanin Sa — Kannywood

Jamilu Dakan Daka


JAMILU DAKAN ƊAKA

Daga : Amira Abubakar daga Kano.


Tun bayan bayyana somin taɓin wasu fina-finai da Kamfanin Al-Mubark Internation suka lasawa ma'abota sha’awar kallon fina-finan Hausa irinsu Adam, Ruɗani da Mutuwar Aure, Jama’a ke ta nuna gamsuwa da kuma yabawa da ƙoƙarin da shugaban Kamfanin Na Al-Mubarak International wanda kuma shi ne shugaban Kungiyar Arewa Film Makers reshen Jihar Kano, sannan kuma Basarake Sardaunan Masana'antar shirya fina-finan Hausa Alhaji Jamilu Ahmad Yakasai wanda aka fi sani da Jamilu Dakan Ɗaka ke jagoranta. Ko shakka babu a cikin waɗannan fina-finai anyi amfani da masu gidan Rana (Kuɗi), gogewa, tsananin sanin siddabarun gamsar da ‘yan Kallo tare dayin ƙoƙarin tallata fasahar masu shirya fina-finan Hausa a Ƙasashen Turai musamman Ingila.

Kamar yadda aka ga irin hazaƙar da aka baje kolinta a cikin fim ɗin Adam, ta yadda zargin niyyar ƙarin aure ya sanya wata mace shirya gidogar hallaka kanta domin kawai ta jefa mijin nata cikin tsaka mai wuya, sannan kuma anga yadda Lauyoyi suka nuna kwarewa da kuma irin cajin kan da aka jefa masu kallo aciki kafin ƙarshen fim ɗin gaskiya tayi halinta. Wannan fim ya tabbatar da kwarewar da aka jima ana kwankwaɗa daga duk wani fim da aka ce waccan kamfani ya shirya. Wannan ya ƙara zama shaida idan aka dubi shirin fim ɗin Mutuwar Aure da kuma fim ɗin Ruɗani.

Ganin yadda yabo da jinjina suka yawaita ga shugaban da ya jagoranci fina-finan Jamilu Dakan Daka yasa Kannywood today yin tattaki har ofishinsa dake Gidan SKY kan titin Zuwa Gidan Zoo inda ya amsa wasu ‘yan tambayoyin mu kamar Haka: Mun fara da tambayarsa inda shari’ar da akaji sun gurfanar da Jaruma Nafisa Abdullahi kan layar zana data a farko ta yiwa fim ɗin Mutuwar aure, sai ya amsa da cewar wannan Magana an sasanta harma tuni ta kammala aikinta, yace wasu muhimman abokan sana’armu suka shiga cikin maganar suka sasanta irinsu Adam A. Zango da sauransu. Haka kuma da yake amsa tambaya kan yadda yake jin yabo daga masu bibiyar fina-finansa musamman yadda fim ɗin Adam ya ya mutsa hazo tare da karɓar yabo da jinjina kan yadda aka shirya fim ɗin, sai yace ina matuƙar farin ciki kuma abin bai zamomin da mamaki ba kasancewar wannan shi ne babban abinda muka ƙuduri aniya na ganin mun sake salon shirya fina-finan mu ta yadda duniya zata amince da kwarewarmu.
DAKA ƊAKA DA NAFISA ABDULLAHI YAYIN DAUKAR FIM

Jamilu Dakan Ɗaka wanda ya godewa jama’a, abokan sana’arsa da kuma mutanen da ke ƙasashen ƙetare da muke aiki tare dasu domin ciyar da wannan masana’anta gaba, yace yanzu haka akwai fim mai suna Ruɗani yana nan kan hanyar fitowa, harda Baturiya acikin fim ɗin kuma ina tabbatarwa da Jama’a cewar shima kamar sauran haka zai kayatar da abokan mu’amalarmu.

A ƙarshe ya miƙa saƙon murnar shiga wannan wata Mai albarka tare da addu’ar fatan Allah ya karɓi ibadunmu. Fina-finan Jamilu Dakan Ɗaka sun zama sha Kallo ga ma’abotan fina-finan Hausa.

Source : KannywoodToday
Tallata wakar ka : Send Email Or Call