Dalilan Da Sukasa Yan Daba Suka Sassari Jarumi Sharif Aminu Ahlan !

Dalilan Da Sukasa Yan Daba Suka Sassari Jarumi Sharif Ahlan

Dalilan Da Sukasa Yan Daba Suka Sassari Jarumi Aminu Sharif Ahlan.

"Miliyoyin mutane a fadin duniya sun ga hotunan da mutane da jaridu suka buga ina jike cikin jini sanadiyyar sara har waje biyar da wasu alzalumai suka yi yunkurin halaka ni. Amma ba wanda ya san zahirin dalilin kisan da aka kusan yi min.

Yau kwana bakwai da faruwar abin, jita jita da shaci fadi kawai ake, wasu su ce sata aka zo yi min. Wasu su ce ai makiya ne da na tsone wa ido. Dalilai barkatai.

GASKIYAR ABINDA YA FARU shine, Ina zaune wajen 11 na dare a kofar gidana da na koma a unguwar Ja'en dake Kano, kusa da layin shago tara. Sai ga mutane tsaye kai na da makamai suka kama sarana, karshe suka ce min sun ga rubuce-rubace na da kuma banner da na yi wa gwamna, wanda M.D na RIWASA ya dauki nauyi. Kuma sun gargade ni cewa nan gaba kashe ka za mu yi. Fitowar mutane yasa suka gudu.

WANNAN SHINE GASKIYA, GODIYA GA JAMA'A MASOYA, MAKWABTA, 'YAN JARIDA DA KOWA DA KOWA", Shariff Aminu Ahlan.

Kalla Cikin Hotuna.

Tallata wakar ka : Send Email Or Call