Rashin Kasuwar Fina-Finai Ke Kawo Ma Kannywood Koma Baya - Mansur SadiQRashin kasuwar fina-finai na kawo wa masana’antar Kannywood koma baya ta inda take dakile kudaden shiga ga masu harkar da ma gwamnati.

Wanna kuma ya kasance kalubalen da ke ci ma masana’antar tuwo a kwarya in ji Mansur Sadiq, wani darakta kuma mai shirya fina finai a kannywood.

Ya bayyana haka ne a yayin da yake zantawa da wakiliyar DandalinVOA Baraka Bashir a garin Kano a yau litinin.

Ya kara da cewa a matsayinsa na wanda ya karanci harkar kasuwanci ya tilasta masa yin rubutu da yake son baiwa haddadiyar kungiyar Kannywood kan hanyoyin da za a bi domin magance matsalar.

Mansur ya ce ya faro harkar fim ne tun daga tushe wato lighta man har ta kai shi ga inda yake a yanzu, kuma ya fara sana’ar ne tun yana dan shekara takwas da haihuwa, inda ya ke cewa babban burinsa dai bai wuce ya tsinci kansa a masanaantar Nollywood ba.
Tallata wakar ka : Send Email Or Call