Nafisa Abdullahi Ta Kafa Sabon Tarihi A Masana'antar Kannywood.

Jaruma Nafisa Abdullahi Ta Kafa Tarihi A Masana'antar Kannywood

Jaruma Nafisa Abdullahi Ta Kafa Sabon Tarihi A Masana'antar Kannywood.

Jarumar ta kafa tarihi a wani sabon Film dinta me suna SULTANA, Wanda daya daga cikin fitattu masu shirya Fina-finan Hausa Abdul Amart Maikwashewa ya Shirya.

Film din SULTANA film ne daya jawo cece kuce tun gabanin a shiryashi sakamakon wadansu irin hotuna da aka yita yawo dasu a kafofin sadarwa dake nuni da cewa Jaruma Nafisa Abdullahi ta aske gashin kanta wanda, kuma a zahiri ba haka bane domin kuwa jarumar ta karyata wannan batu.

Sultana Hausa Film


Kuma  Film Din Sultana dai fim ne da ya kunshi shahararru kuma jaruman ‘yan fim da ya hada da Jaruma Nafeesat Abdullahi, Wannan fim dai anayi masa kirari da ‘Kamar Ba A Taba Yin Irinsa Ba’ tun kafin ya fito ganin irin jaruman da suka fito a fim din.

Jaruman da suka fito a fim din sun hada da Sarki Ali Nuhu, Wassh Waziri,Hauwa Maina, Adam Zango da dai sauransu.

Jarumar kuwa tabar tarihine bisa irin na mijin kokarin da tayi a wannan shiri da kuma jarumtaka wajan fitowa a film din da wata kalar siffa mai ban mamaki data GirGiza ma'abota kallon Fina Finan Hausa.
Tallata wakar ka : Send Email Or Call