Wani Matashin Mawaki Dan Nigeria Ya Lashe Gasar Mawaka A Ingila

Th Voice UK MO Adeniran


Wani Matashin Mawaki Dan Nigeria Ya Lashe Gasar Mawaka A Kasar Birtaniya Ingila.


Daga : Dandalinvoa.

Haifaffen Najeriya Mo Adeniran, ya zama zakara a gasar mawakan kasar Ingila. ‘The Voice UK’ Matashi mai shekaru 21 da haihuwa, yana aikin dare a wani Otel, don samun abun dogaro da kai.

Ya shiga gasar mawakan kasar Birtaniya, inda ya lashe gasar. Shidai ba mawaki bane amma yana da sha'awar waka.

Adeniran, yayi rayuwar shi a gidan marayu, kasancewar ya rasa iyayen shi. Kana ya rasa wani daga cikin abokan shi, sanadiyar shaye-shaye.

Matashin ya taka rawar gani matuka wajen lashe gasar, biyo bayan wasu zakaru da ya doke don samun nasara.

Mutane a kasar Britaniya, sun kada kuri don zaben wanda zai shiga zagaye na kusan karshe, inda yayi nasara biyo bayan zaben da aka yi mishi.

Masoya wannan wasan sun kara son mawakin dan Najeriya, dalilin wata waka da ya raira ta wani tsohon mawakin kasar Sam Cooke.
Tallata wakar ka : Send Email Or Call