Wakokin Hausa Hip-Hop Zasu Mamaye Duniya Bada Jimawa Ba.

 Wakokin Hausa Hip hop


Wakokin Hausa Hip-Hop Zasu Mamaye Duniya Bada Jimawa Ba.

Bello Ibrahim Billy O.

Babban kalubalen da harkar Hip Hop ke fuskanta a kasar Hausa, bai wuce rashin samun kamfanin da ke dillanci mawaka wajen daukar sauti, tallatasu da ma kasuwancin wakar da suke yi, a cewar shahararren mawaki, marubuci "Billy O".

Bello Ibrahim "Billy O" ya ce kawo yanzu dai, al'ummar kasar Hausa sun karbi wakar Hip-Hop ta Hausa, fiye da yadda aka karbi wakokin soyayya da ma na nanaye.

Ya ce abin takaici ne yadda gwamnmati bata maida harkar wakar Hip Hop da muhimmanci, a matsayinta na hanyar samar da kudaden shiga ga kasa, da kara karfafama matasa.

Ya ce a yanzu an kara samun wayewa, kuma ana karbar harkar ta inda duk wani matashin da ya tashi a yanzu, kuma yake harkar waka toh lallai ya fi zabar bangaren Hip-Hop ne.

Ya ce wakar Hip-Hop ta fi yiwa wanda yayi karatun boko adon, a cewarsa wakar na tafiya da boko, domin waka ce da ake yinta ta hanyar yin yanga a salo da yadda ake rereta.

Billy O, a yanzu dai Hip-Hop ta samu karbuwa domin har kananan matasa sun fara karbar ta, don nishadantarwa da ilmantar da sauran matasa.

ku biyo mu domin jin cikakkiyar hirar mu da jigo a harkar Hip-Hop "Billy O" dangane da matsayin wakar Hip-Hop da kuma wasu daga cikin kalubalen da suke fuskanta.

Domin Sauraro Firan Cikin Sauti Zaku Iya Download Dinshi Gashi.

Download Audio Now

© Dandalinvoa
Tallata wakar ka : Send Email Or Call