Nafisa Abdullahi Ta Jefa Guri'ar Kin Amincewa Da Dawo Da Rahama Sadau Kannywood

 Rahama Sadau

Fitacciyar Jarumar Shirin Fina-finan Hausa Na Kannywood Nafisa Abdullahi Ta Jefa Guri'ar Kin Amincewa Da Dawo Da Rahama Sadau Kannywood Industry.

Kome Yasa Hakan ? Gadai Abinda Jarumar Ta Fada Da Kuma Dalilan ta Nayin Hakan.

Acewarta idan aka dawo da ita an nuna son kai, Domin ashekarun baya an kori jarumai irinsu, Kubura Dako, Safiya Musa, Maryam Hiyana, Ummi Nuhu da sauransu, amma har yanzu ba’a dawo da su ba. Har wasu suka yi aure. Inji Nafisa Abdullahi.

Sannan a daya bangaran kuma Jarumi Sani Danja shine kan gaba, inda ya kada tasa Guri'ar domin nuna Amincewa da dawo da Rahama Sadau.

Sani Danja yace masana’antar kannywood ta sami koma baya tun bayan da aka kori Rahma Sadau. Domin Rahma jarumace mai tarin masoya a Arewaci da kudancin kasar nan.

Duk da yake Rahma tayi laifi kuma ta amsa tayi laifi, ya kamata a yafe mata. Domin mu ma muna yiwa Allah laifi kuma ya yafe mana. Inji Sani Danja.

Shin ko mene ra'ayoyin ku game da wannan batu da yanzu haka ake kan ci gaba da kada Guri'u. ??Tallata wakar ka : Send Email Or Call