Mawaki Nura M Inuwa Zai Angon Ce A Ranar 29/04/2017

Nura M Inuwa Aure

Mawaki Nura M Inuwa Zai Angwance A Ranar 29th Ga Wannan Watan Da Muke Ciki Wato 29/04/2017  April. Tare Da Amaryar Sa Malama Amina.

 Nura M Inuwa Ango


Dama Hausawa sunce sannu sannu bata hana zuwa sai dai a dade Ba'a Jeba.

Kuma dama wannan na daya daga cikin babban abinda dubban masoya suka dade suna jira, musamman idan mutum yana yawan bibiyar shafukan sada zumunta, cikin zaurukan da Masoyan Nura M Inuwa suke mu'amalanta to zaka yita cin karo da zantuka maban banta akan cewa Nura M Inuwa yaki Aure.

Haka shima a nashi bangaran sautari cikin wasu wakokin sa ya kanyi habaici da fadin cewa Aure Lokaci ne.

Domin haka kuci gaba da kasancewa tare da wannan shafi namu mai tarin Albarka domin kawo muku dumbin hotuna gami da bayanan irin wainar da za'a toya a wannan rana.

Tallata wakar ka : Send Email Or Call