AUDIO : Tattaunawa Kai Tsaye Da Mawaki Sayyad Gadankaya.

 sayyad Gadankaya

AUDIO : Tattaunawa Kai Tsaye Tareda Mawaki Sayyad Gadan Kaya Kano. Kamar Yadda Kuka Sani ne Cewa Wannan Shafin Namu Ya Dade Yana Kawo Muku Wasu Daga Cikin Wakokin Wannan Matashin Mawaki.

Ga Dai Abubuwan Da Mawakin Ya Fadi Kamar Haka Cikin Wannan Tattaunawa.

Sayyad Gadon-Kaya: Sakonnin Da Nake Aikawa Ta Hanyar Waka Na Taka Rawar Gani.

Sai dai babban kalubalen da na ke fuskanta bai wuce yadda wasu daga cikin masoyana ke kira akai-akai bila adadin a lokaci guda, batare da li’akari da yanayin da mutun ke ciki ba inji mawaki Umar Sayyidi Gadon-kaya.

Matashin mawakin da ya samu lambar yabo ta girma wadda ake ba shahararrrun mawaka masu tashe a jihar Bauchi,

A shekarar da ta gabata ya ce yawan kiran da wasu daga cikin masoyansu ke yi yana ci musu tuwo a kwarya domin basa li’akari da cewar ba a kowanne lokaci ne suke samun damar daga wayoyinsu ba.

Daga karshe yayi Karin bayanin cewa a halin da ake ciki, yanzu burinsa ya cika domin kuwa, a mafi yawancin lokuta ya kan samu wayoyin wasu daga cikin masoyansa da kan kira domin bayyana masa irin yadda sakonninda yake isarwa ta hanyar waka na sa wasu da dama canza halayensu.

Domin Sauraro Ciki Audio Sai Kuyi Download Gashinan Daga Kasa.

Ayi Sauraro Lafiya.

Tallata wakar ka : Send Email Or Call