Kannywood Zata Yi Maganin Masu Kutse Cikin Ta.

Ali


Masana'antar Shirya Fina-finan Hausa Na Kannywood Ta Kaddamar Da Kwamitin Yaki Da Masu Kutse Zuwa Masana'antar.

Kamar yadda daya daga cikin manyan jiga jigan hukumar dake sa ido akan Fina Finan Hausa Na Kannywood ya bayyana a cikin wata tattaunawa da yayi da gidan jaridar Voahausa.

Abdallah Tahir Ahmad Alkinana : Mataimakin shugaban kungiyar masu shirya Fina-finan Hausa, kuma wakili a kungiyar Moppan.

Al kinana yace.! wannan dabi’ar na da mummunar illar ga harkar fina-finai wanda a wancan lokacin ba’a sanya kwararan matakai ba na dakile matsalolin, a yanzu kuwa an kafa kwamiti da ke zagawa duk inda ake daukar fina-finai a fadin jihar Kano domin tantancewa tare da tabbatar da cewar ba’a dauki jarumi ko jaruma a bayan fagge ba .

 Ya ce duk wanda ya karya doka za’a dakatar da fim din ko kuwa ya zame wa mai fim din asara, ya kuma kara da cewa a fim din sa da mai Suna ‘Kukan Karshe’ yake yi a yanzu ya tabbatar bai sanya waka tsakani saurayi da budurwa ba kasancewar ana son kawo canji ga masana’antar fina-finai.

Inda yake cewa babban dalilan da yasa sukan sa raye-raye domin masu shirya fim sun lura masu kallonsu abu ne da suke so.Tallata wakar ka : Send Email Or Call