An Gurfanar Da Jaruma Nafisa Abdullahi A Gaban Kuliya.

 Nafisa Abdullahi

NAFISA ABDULLAHI DA JAMILU DAKAN ƊAKA

Sharfuddeen Baba.

Ranar Juma’ar makon daya gabata ne aka sa ran bayyanar Jaruma Nafisa Abdullahi gaban Kotu ta 33 dake zamanta a Unguwar Dorayi dake Birnin Kano. An dai gurfanar da Jarumar ne bisa zargin daina halartar ɗaukar fim din MUTUWAR AURE Wanda Kamfanin Almubarak International Fim Production ke ɗaukar nauyin shiryawa.

Ana zargin Jaruma Nafisa Abdullahi da daina ci gaba ɗaukar shirin fim ɗin, a cewar Jamilu Ahmad Yakasai shugabata Kamfanin Almubarak International Fim wanda shi ne Production, Nafisa Abdullahi ta daina
zuwa wurin ɗaukar shirin wanda anyi nisa da ɗaukar fim, yau sama da wata tara ke nan amma Nafisa Abdullahi ta daina zuwa ba tare da bayar da wani dalili ba. Hakan tasa aka gurfanar da ita gaban kotu mai lamba 33 dake Dorayi, amma ranar da aka shirya fara sauraran kara taki halartar zaman kotun, saboda haka yanzu ana shirin ɗaukar matakin da ya kamata inji Dakan Daka.

Duk kokarin jin ta bakin Jarumar ya ci tura kasancewar layukan da muke dasu nata duk sun kasance a rufe har zuwa hada wannan rahoto.

Daga Shafin :- Kannywood today.Tallata wakar ka : Send Email Or Call