Wakar Abdul D One Abun Da Yake Raina

Abdul D One Abun da Yake Raina

Abdul D One Abun Da Yake Raina Mansoor


Wakar "Abun Dake Raina" Dayace daga cikin wakokin Album din NA RIKE SO Wanda Umar M Sharif ya fitar a karshen shekarar data wuce 2016.

Wanda Album din ya kunshi wakokin mutane uku na farko. Umar M Shareef, Muhammad Melery, Abdul D One.

Muhammad Melery, Da Abdul D One, dukan su matasan mawakan hausa ne masu tasowa wadanda suke a karkashin tutar mai gidan su Umar M Shareef.

Hasalima ba kowa ke iya banbance tsakanin wakokin da suka rera,  da wadanda mai gidan su ya rera ba.

Kuma yanzu haka ma jarumi Ali Nuhu na nan yana shirin fitar da wasu fina finai guda uku wadanda ko wannen su akwai wakar Abdul D One a ciki.

Sannan biyu daga cikin fina finan an samo sunan sune daga sunan wakokin Abdul D One din kamar wakar .. Abun Dake Raina, Da kuma, Abokanai na.

DOWNLOAD : Abdul D One Abun Dake Raina Song.Domin tallata Wakar ka Album ko Video, Aika mana da sako yanzu haka ta hanyar Email

This is an email link: Send Mail