LYRICS: Nura M Inuwa Kidan Samari Lyrics Song

 Nura M Inuwa Kidan Samari Lyrics Song

LYRICS: Nura M Inuwa Kidan Samari Lyrics Song


BAITUKA...

Nura :- Ku matso kuji ga kidan Samarii, talge ai dole sai da garii, wa zayabi tawwagar tsurarii, inna gaji ku kuke da Ganin, kallon ku nake ina tunanii, ku zaku rakani inda zanii.

kudai gaba duniya matasa za'ayyi abunda kunka amsaa, kun gagara ko fage na gasaa.

A cikinmu mu fidda 'yan barandaa, domin rayuwa tana ta tsadaa, me kaudi za' a cewa Sudaa, doki na kara sunansa dandaa fatar akuya ai bata gandaa.

Misali naku dai da hantsii, abin mora ya wucce watsii, a firgita in kukkayi motsii.

Tunkwal tunkwal dakan tabare, tiles a saki da kunyi bore. Yau tazo gobe mui jirantaa, ruwa ke maganini kazantaa, domin lada akanyi bautaa, komai sai daku an amintaa, Allahu ya amshi addu'ataa.

Kuma farga mu hadda kawunan mu, daga ranar mun kashe kishin mu.

Mu dai na shiga mota ta alfaa, ta ajemu gurin da babu Rumfa.

Ga maliya duk mu kyala radii, sanda itace idan makafii, in kun tsuma duk ku bani tafii.

Yau ba'a duba matstsalar ku, ku dunga tuno hakan a ranks, ku wakalta ba ayin biyanku.

Sai dai a saka ku tashi zugaa, shedan kuma na buganku gangaa, in Anka biyo ku sai ku rugaa, sanadi na gudu ku yaga rigaa, wani ma ya duro takan katangaa.

Ko yin haka gunku fa idane ? A gurin jama'a kuwa matstsala ne, manya kuke gobe gun Mutane.

Jinka a dagata sai da taroo, tambihi zamu yiwa yaroo, tsaya da kafa ka fidda tsoroo, jajirce ai kiranka toroo, feshi illa yakewa kwaroo.

Kambunku kusa haha mazaje, a jikinku ku karkade kudaje.

A zamani kun zamo kujeraa, sai an tafiya daku ku Luraa, me muzanta ku kyan shi koraa, bazan tufka da warwara baa, rago bazai yi dammara baa.

Me kwantsa a ido yaje ya wanke, me barci bai wuce na farke, me yin dunkum be kyau da aike, me jin tausai ke share kuke.

Ni duniya ta isan karatuu, kowa ya biye ta zaya cutu.

Mu bita da kyau sabo da Zargii, Qurji meshi ya kanji zugii, ga kauraye da masu dannii, tururuwa itta keda dangii.

Kar kuce baku issa maggana baa, in baku su basa haye baa.

Kuke kawo sabon tunani, yayi amfani cikin sakon ni,  layin ku nake nima ku ganni, bana san masu bani bani.

Karfin ku a yanzu yai isowaa, ragama ya kamata kui rikewaa.

Komai ku shigo daku a dama, rigar 'yanci da kai ku nema, nauyinku ku bar azawa Mama, kuji masu ado da gyara Suma, kallo bai wa ido yawa ba, kune kune zaku tallafawa Baba, tunkahon al'umma matasa, wannan lokacin kune Samari.

Domin tallata Wakar ka Album ko Video, Aika mana da sako yanzu haka ta hanyar Email

This is an email link: Send Mail