LYRICS: Nura M Inuwa Best Of Dan Magori Lyrics

Nura M Inuwa Best Of Dan Magori Lyrics

LYRICS: Nura M Inuwa Best Of Dan Magori Lyrics

Nura :- Taka rawar gani a kalla komai kai kanka duniyace mai jimurin zama cikin ta shike zuga kansa dan magorii.

AMSHI :- Taka rawar gani a kalla komai kai kanka duniyace mai jimirin zama cikinta shike zuga kansa dan Magori (x2).

Nura :- Nadau kallami da warrakata zan dukkufa ne wajan rubutuu, jahilci na kirashi cuta 'yan yara muje muyo  karatuu, kwando bazai rike ruwa ba madadin sa sai a dauki kuttuu, domin kuwa sai ga mai idanu banbance gyadar gwarai da bori.

AMSHI :- Taka rawar gani a kalla komai kai kanka duniyace mai jimurin zama cikin ta shike zuga kansa dan Magori.

Nura :- In kaji ga ki gudu sai in sa gudu bai iso wurin baa, dukan gero ku killace ta tsabar ce zata bada gumbaa, zancena kar naja da nisa yan yatsu suke da kumbaa, nafi gane abin da ban sani ba in tambayi yan maza na daurii.

AMSHI :- Taka rawar gani a kalla kome kai kanka duniyace mai jimirin zama cikin ta shike zuga kansa dan Magori.

Nura :- Ruwa ne maganin kazanta baya kyale wuta ta ruru, mai yin tafiya da duba bayaa yana da wahala ya biggi garu, mai hauka inya fara duka daureshi a sa a turu, me cin kasa gargadi ake mai yabi sannu kar ya dau ta shurii.

AMSHI :- Taka rawar gani a kalla kome kai kanka duniyace mai jimirin zama cikin ta shike zuga kansa dan Magori.

AMSHI :- Taka rawar gani a kalla kome kai kanka duniyace mai jimirin zama cikin ta shike zuga kansa dan Magori.

Nura :- Kishiya itace ka sanya mata kidima harma su kasa guda, zafi inya shige kwakwalwa seta fara kuda, girman san dan rake ga kallo a idanu ya wuce takanda, cin hakin sama kyau a barwa tsuntsu,  na cikin kunga kyansa kwarii. 

AMSHI :- Taka rawar gani a kalla kome kai kanka duniyace mai jimirin zama cikin ta shike zuga kansa dan Magori.

Nura :- Daidan wani zaya bashi daidai a wurin wani kumma karkata  ne, gaskiya dauko kasa gabanka karka damu da ra;a'ayin mutane, duba ko bangaran abincin ka gurin wani tabbata guba ne, kamar kura nama take so, akuya kuwa se dai ta kurbi tsarii.
AMSHI :- Taka rawar gani a kalla kome kai kanka duniyace mai jimirin zama cikin ta shike zuga kansa dan Magori.

Nura :- Inkayi abun ayo yabon ka zaa ai koda bakaffadi ba, sakon da ake bida da sauri ba a baiwa marar kafa ba, tashi da kaga anayi bazai yuwu ba da fiffike ba, riko na gida a baiwa babba yaro aka bashi yayi zarii. 

AMSHI :- Taka rawar gani a kalla kome kai kanka duniyace mai jimirin zama cikin ta shike zuga kansa dan Magori.

Nura:- Taka rawar gani a kalla kome kai kanka duniyace mai jimirin zama cikin ta shike zuga kansa dan Magori.

AMSHI :- Taka rawar gani a kalla kome kai kanka duniyace mai jimirin zama cikin ta shike zuga kansa dan Magori.

Saukar Da Audio Nura M Inuwa Best Of Dan Magori Album.

Domin tallata Wakar ka Album ko Video, Aika mana da sako yanzu haka ta hanyar Email

This is an email link: Send Mail