MUSIC: Nura M Inuwa - Ankon Biki

Nura M Inuwa Ankon Biki

MUSIC: Nura M Inuwa - Ankon Biki


Saukar da sabuwar wakar Nura M Inuwa mai suna "Ankon Biki.

Kadan daga cikin baitukan da wakar ta kunsa.

Nura :- Ranar shagali mata sai kui shigarku ta alfarma, Anko na biki ku sako dan yafi kyau da bikin girma.

AMSHI :- Ranar shagali mata sai kui shigarku ta alfarma, Anko na biki ku sako dan yafi kyau da bikin girma (x2).

Nura :- Komai zai sa kuka bai kai rabo da masoyi baa, zaman duniya dadi in baka tara magautabaa, duk da na kwarai shine baza yayarda iyaye baa, Mata kuyi yanga ballagaza ku barta wurin gulma.

AMSHI :- Ranar shagali mata sai kui shigarku ta alfarma, Anko na biki ku sako dan yafi kyau da bikin girma.

Nura :- Farar aniya laya kwarya ko sai ta biye kwaryaaa, ranar murna tazo dangi kuzo mubi Soyayyaa, ana maganar gata bora tana a sahun baya. 

AMSHI :- Ranar shagali mata sai kui shigarku ta alfarma, Anko na biki ku sako dan yafi kyau da bikin girma.

Nura :- Kuna buduri nazo kowa yana taku daidai.

AMSHI :- Aure

Nura :- Kawaye sun sanyo anko shigar da sukai daidai.

AMSHI :- Aure

Nura :- Amarya yar gata ki fito jiran ki ake ke dai.

AMSHI :- Aure

Nura :- Anko na bikin ki yana sheki ango yana ya tsaya dama.

AMSHI :- Ranar shagali mata sai kui shigarku ta alfarma, Anko na biki ku sako dan yafi kyau da bikin girma.

Domin tallata Wakar ka Album ko Video, Aika mana da sako yanzu haka ta hanyar Email

This is an email link: Send Mail