[Lyrics] Umar M Sharif “Hasashe” Lyrics Song

Umar M Sharif Hasashe Lyrics Song

[Lyrics] Umar M Sharif Hasashe Lyrics

#Hmn ! Nai Hasashee Hasashee

-Hasashena ya tabbata gamu a tare cikin soyayya, In bake sena jikkita; yaki taho zo muyi tarayya.

#Hasashena ya tabbata gamu a tare cikin soyayya, Inba kai sena jikkita yaka taho zo muyi tarayya.

-Hey tafiya sannu sannu ake farawa, dokin hakuri duk wanda ya haushi yana dacewa, a tsakani indai an zauna akan sabawa, in an sasanta dai dai ne shine more wa, kaina na baki,  na zam naki,  kallan da idanunki,  ya sakan shauki.

#Kai zan ba zobe ka sakashi a hunnunka, ban fatan mu rabe ka sakani a kirjinka, kai na kira gwadabe ka bani takobinka, inka ban zani cafe, amman sena doka; biyayya zan nuna 'kullum in gaisheka, na barsu mahaifana, na yarje zan bika.

-Hasashena ya tabbata gamu a tare cikin soyayya, In bake sena jikkita; yaki taho zo muyi tarayya.

-Ta dabance ke ta daban,  a ciki kena ware. Ku rabamu kunyi kadan, in kunka matsa se kun siare, mutuwace ni zanyi idan babu ke sena haure,

lafiyata kece indai babu ke fa kwarai bani, na tsaya na nace lallai bani gudu se an bani, a bari yahhuce shike bada rabo ga wani.

#Hasashena ya tabbata gamu a tare cikin soyayya, Inba kai sena jikkita yaka taho zo muyi tarayya.

-Hasashena ya tabbata gamu a tare cikin soyayya, In bake sena jikkita; yaki taho zo muyi tarayya.

#Ni taka tun asali ba me kwacema, zana sako kwalli inzo innuna ma, kai ka sakani kiba jikina ba rama, hankalina ya kwanta, damuwa tuni na manta da zuwanka cikin rai na.

-Idan gaki,  ba watta macce da zan kalla, 'Diya babba yar makaranta ba kiyin talla, tafiyata mai nisa a gidanki zan billa, kin koremun komai ze sani nai kwalla.

Hasashena, tunanina, tanuna manuniya gakinan ganii.

#Hasashena ya tabbata gamu a tare cikin soyayya, Inba kai sena jikkita yaka taho zo muyi tarayya.

Domin tallata Wakar ka Album ko Video, Aika mana da sako yanzu haka ta hanyar Email

This is an email link: Send Mail