LYRICS: Nura M Inuwa Dashen Jini Lyrics

LYRICS: Nura M Inuwa Dashen Jini Lyrics

-Jinin mu yayi dashe da kauna, Zuciya tuni ta amince dani dake bama rabewa.

#Jinin mu yayi dashe na kauna,  zuciya tuni ta amince dani da kai bama rabewa.

-Babu tababa hakika dashen jini ke sanya kauna, Zuciya se ta amince so ya samu wuri ya zauna, Soyayya inta bunkasa sai a rinka kama da juna, Damina Inhar ta sauka furan yabanya zai fitowaa.

-Jinin mu yayi dashe na kauna so ya samu wuri ya zauna. - Zuciya tuni ta amince dani dake bama rabewa.

#Na yiyo damara a kaunarka zuciyata ta amince, Kyan halinka yasa a kullum dakai nake so in kasance, Kalleni nazam madubinka in kamun haka nayi dace, Na bude zuciyata sanka nasa ciki nai rufewaa.

-Da alama nayi dace ni kika ba kambu na kauna, Taimako yau_yai minni rana, yau na samu farinciki na, Zahiri nayyo maraba dake abun da nasa a raina, Zan alfahari na gammu a rayuwa mai dorewaa.

-Jinin mu yayi dashe da kauna, Zuciya tuni ta amince dani dake bama rabewa.

#Jinin mu yayi dashe na kauna,  zuciya tuni ta amince dani da kai bama rabewa.

#Marhaba bika ya masoyi zanyi kiran ka muradina, A raina nayima muhalli na sani kasan nufina, Bani sauraran waninka bare yace in bashi kauna, Nayi alkawari da kai na kai zan bawa dukan kulawaa.

-Shi zama da wanda kake so a duniya dadi yakeyi, Kin bani so kuma nai rikewa baba zancan kani kayi, Turbar dana hau na zauna ta hanani nayo bulayi, Nayi saka harda tufka kar in sake tai warwarewaa.

#Jinin mu yayi dashe na kauna. - Zuciya tuni ta amince dani dake bama rabewa.

#A jininmu abun yake ne; to naji dadin mallakar ka, Na fada maka sirrika na; fadarka anan na sauka, Ni nayi dammara ne zana kare martabar ka, Jarumina ginshiki na a gareka ina yabawaa.

-Jinin mu yayi dashe da kauna, Zuciya tuni ta amince dani dake bama rabewa.

#Jinin mu yayi dashe na kauna,  zuciya tuni ta amince dani da kai bama rabewa.

Domin tallata Wakar ka Album ko Video, Aika mana da sako yanzu haka ta hanyar Email

This is an email link: Send Mail