[Lyrics] Nazeer M Saulawa Karfafamin Zuciya Lyrics

Nazeer M Saulawa Karfafamin Zuciya lyrics

[LYRICS] Nazeer M Saulawa Karfafamin Zuciya Lyrics Song


~Inada buri zuciya amma bazan furta ba ~Inata farautar cigaba haryau ban cire buri ba

~Cikin raina ga fargaba amma ban karaya ba ~Tunanina ya zurfafe ina hangen nasara gaba. Eh...

Karfafamin zuciya, Tsarkakemin zuciya, Karfafeni Rabbana inyi dogaro dakai.

A koyaushe zan fadi zance bani sakin linzamina Inwa kaina takunkumi don kar inyi aman barna Tunani inya shigo kaina sai in dau alkalamina Daukaka ta rabbi ce ba nufin waninsa ba. 

~Kodayaushe zuciyata waka na cike a raina ~Rabuwar mahaifiyana shiya zama sanadina ~Sai in ringa rera wakar don in tausa zuciyana

~Tun ina kuruciyata buri ban rabu dashi ba.

~An ce dukkan so so ne kowa baiki kansa ba

~Laifuka na tattara banso nai dakonsu ba

~Mai hangen laifin wani bazai hangi nasa ba

~Rabbi tsareni da yin aikinda bazaka so shi ba.

~Rayuwarnan jarabawa ce wallah na sani

~Wani yana neman samu wani ya samu tuntuni

~Sai an jure bakar wuya sannan a zamo gwani

~Sannu sannu faduwa zata zama cigaba.

~Kai kuji halin zuciya mai sas saka lamari

~Duk sanda ta yunkuro sai in dinga nazari ~Ni bazan biye sonkai ba don yanada hadari ~Yauda gobe watakil rabo yana zuwa gaba.

~Ga Allah rabbi nake roko ba gun wani bawa ba ~In kuma kaban na karba baiwuce ikon Allah ba ~Bazanwa wanina hassada ba don bani na bashi ba ~Yau da gobe wataranma bazaku ganni ba.Tallata wakar ka : Send Email Or Call