[Labari] Rahama Sadau Ta Amsa Gayyatar Mawaki Akon

Rahama Sadau Tare Da Akon

A Yaune Daya Daga Cikin Shahararrun Yan Wasan Hausa Film Kuma Jaruwa A Fagen Shirya Fina-finan Hausa Na Kannywood Wato Rahama Sadau Ta Amsa Gayyatar Shahararren Mawakin Nan Na Kasar Amurka Haifaffen Kasar Senigal Wato Akon Tareda Shugaban Sashen Shirya Fina-finai Na Hollywood Wato Jeta Ameta Sukayi Mata A Shafukan Su Na Twitter.

Rahama Sadau A America

Hakan Kuwa Ya Farune Tun Biyo Bayan Koran Da Hukumar Dakesa Ido Akan Harkokin Tace Fina Finai Na Kannywood Wato MOPPAN Tayi Mata A Sana Diyyar Wani Faifan Video Data Dauka Tareda Wani Matashin Wakin Hausa Hip/Hop Mai Suna ClassiQ Dan Asalin Jihar Bauchi Inda Jarumar Ta Rungume Shi A Cikin Videon.


[VIDEO] Download Classiq Ft Avala With Rahama Sadau I Love You...


Wanda Hakan Ya Jawo Cece Kuce Musamman A Shafukan Sada Zumunta Na Facebook, Twitter, Whatsapp Wanda Da Yawan Mutane Ke Ganin Ya Sabawa Addininta Da Kuma Aladarta Ta Bahaushiya.


Ta Yadda Yanzu Haka Ake Ci Gaba Da Tafka Muhawara Musamman A Shafukan Sada Zumunta, Ta Yadda Wasu Ke Ganin Cewa Jaruma Raham Sadau Ta Tafka Babban Kuskure Bisa Amsa Wannan Gayyatar Da Tayi Sakamakon Irin Kiraye Kirayen Da Wani Babban Shehin Malami A Jihar Kano Yayi Mata Wato Sheikh Malam Aminu Ibrahim Daurawa.

Amma Sai Gashi Jarumar Ta Kekashe Kunnuwarta Ta Shilla Zuwa Kasar Amurka Domin Amsa Wannan Gayyata.

MENE NE RA'AYOYIN KU AKAN HAKAN ??Tallata wakar ka : Send Email Or Call